Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada belin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore. Alkalin kotun ya gindaya masa sharudda.
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada belin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore. Alkalin kotun ya gindaya masa sharudda.
Bayan shekaru 50, gwamnatin tarayya ta yi wasu gyare-gyare a tsarin NYSC. Sabon tsarin ya zo da rage karfin sojoji, kokarin koyar da sana'o'in zamani da kyau.
Babban Hafsan Sojoji a Najeriya, Manjo Janar Waidi Shaibu, ya umarci sojojin Operation FANSAN YANMA su tashi tsaye wajen ceto daliban GGCSS Maga da aka sace a Kebbi.
Rikicin tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose da Olusegun Obasanjo ya dawo sabo 'yan sa'a'i bayan sun yi sulhu. Fayose ya yi wa Obasanjo maganganu masu zafi.
Yan kasuwa da masu ruwa da tsaki a harkokin noma sun jinjina wa gwamnatin tarayya bisa yadda tsadar kayan abinci ke kara a jihohi iirinsu Kwara, Ogun da Oyo.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan matsalar rashin tsaro. Ya gayawa Shugaba Bola Tinubu hanyar shawo kan matsalar.
Majiyoyi sun tabbatar da mutuwar Christopher Igwe, dan'uwan kwamishinan Ebonyi, bayan wasu ’yan fashi sun bude wuta suka harbe shi yayin wani da ake zaman makoki.
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kashe wani jami'in sojan saman Najeriya a jihar Legas. Wani mutum da ake zargi yana da tabin hankali ne ya kashe sojan.
Kungiyar gwamnonin Arewa ta yi magana kan dalibai mata 25 da aka sace a jihar Kebbi. Gwamna Inuwa Yahaya ya ce ba za a lamunci barazana da ilimi ba.
A labarin nan, za a ji cewa jami'an tsaron jihar Katsina sun yi nasarar ram da wasu mutane guda hudu da suka tabbatar da cewa sun mika bayanan sirri ga 'yan ta'adda.
Dan majalisar Amurka, Riley Moore ya ce ya san a yankin Kiristoci aka sace daliban GGSSC Maga a jihar Kebbi. Bashir Ahmad ya masa martani kan kuskuren da ya yi.
Labarai
Samu kari