Wasu magoya bayan jam'iyyar APC sun yi zanga-zangar adawa da kakaba 'yan takara da suka ce an yi kafin zaben fitar da gwani. Sun yi fashe-fashe a zanga-zangar.
Wasu magoya bayan jam'iyyar APC sun yi zanga-zangar adawa da kakaba 'yan takara da suka ce an yi kafin zaben fitar da gwani. Sun yi fashe-fashe a zanga-zangar.
Shugaba Bola Tinubu ya nada Adedayo Laniyi a matsayin shugabar cibiyar Maryam Babangida ta bunkasa mata tare da kafa sabuwar majalisar gudanarwa.
Hukumar tsaro ta farin kaya ta gurfanar da mutumin da ake zargi da safarar makamai ga 'yan bindiga a jihar Kano. Mutum bai amince da laifinsa ba yayin zaman kotun.
Gwamnatin Tarayya ta shirya dira kan 'yan Kirifto da ke harkokin kasuwanci ba bisa ka'ida ba a kokarin inganta darajar Naira saboda farfaɗo da tattalin arziki.
Babbar kotun jihar Ekiti ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu 'yan fashi da makami guda uku. Kotun ta ce an yanke musu hukunci ne bayan kama su da laifi.
Gwamnatin jihar Kano ta bude littafin yin rajistar adadin mamatan da ake binnewa a makabartun domin taimaka mata wajen tattara bayanai, inji ma'aikatar lafiya.
Gwamna Siminialayi Fubara na jihar Rivers ya yi barazanar wofantar da 'yan majalisar dokokin jihar yana mai cewa wanzuwar ‘yan majalisar ta ta'allaka ga amincewarsa.
Rahotanni daga ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna sun nuna yadda jama'a suka haƙura da zama a gidajensu saboda yawaitar hare-haren ƴan bindiga a kauyuka 10.
Bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi sun sake bullo da cajin kudaden ajiya ga daidaikun mutane da da kamfanoni a fadin kasar bayan wa’adin da aka diba ya kare.
'Yan Najeriya za su fara biyan harajin tsaron yanar gizo na kaso 0.5% daga dukkanin kudaden da za su rika turawa ta yanar gizo. CBN ya ba banuna umarnin cire kudin.
Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya soke tafiyar da aka tsara zai wakilci shugaba Tinubu a taron kasuwanci tsakanin Afirka da Amurka a Dellas.
Labarai
Samu kari