Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Lokoja na jihar Kogi, ta sauya janye hukuncin da ta bada na tilastawa hukumar INEC yin rajistar jam'iyyar NDC.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Lokoja na jihar Kogi, ta sauya janye hukuncin da ta bada na tilastawa hukumar INEC yin rajistar jam'iyyar NDC.
An samu rahoton cewa mutane da ke aiki da Sunday Igboho domin farautar 'yan bindiga sun hadu da fushin 'yan bindiga. An yi wa mutanen Igboho jina-jina.
Kungiyar Kwadago a Najeriya ta yi magana kan shirin zanga-zanga da ake yi a kasar inda ta ba Shugaba Bola Tinubu shawarar yadda zai dakile shirin.
Hafsun sojojin Najeriya, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya bayyana hakar ma'adanai da satar shanu cikin manyan abubuwan da ke kawo cikas wajen yakar yan ta'adda.
Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya gayyaci shugabannin matasan da ke shirin yin zanga-zanga a fadin kasar.
Gwamnatin jihar Zamfara ta yi martani ga Bello Matawalle inda ta tabbatar da cewa babu abin da zai saka ta zaman tattaunawa da 'yan bindiga saboda ba mafita ba ne.
Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da matakin da kwamishinan wasanni ya ɗauka na raba gari da shugabannin rikon kwarya a kungiyar kwallon ƙafa ta Kano Pillars.
Kungiyar matasan Arewa ta janye shirinta na zanga-zanga inda ta ce akwai lauje cikin nadi daga Kudancin Najeriya domin kawo rigima a Arewacin Najeriya.
Fitaccen lauya mazaunin jihar Kano, Umar Sa'ad Hassan ya yabawa matakin kirkirar masarautu guda uku masu daraja ta biyu da Gwamna Abba Kabir ya yi a jihar Kano.
Wasu gungun matasa da ake zargin magoya bayan tsohon sarkin Kano Aminu Ado Bayero ne sun farmaki ɗan majalisar Gwale a wurin taron saukar Alkur'ani.
Kotun daukaka kara mai zama a Lagos ta tabbatar da hukuncin da aka yankewa Baale na Shangisha, Magodo, ta rage masa shekaru 3 daga cikin shekaru 15.
Labarai
Samu kari