Shugaban INEC Ya Gamu da Matsala a Kasar Waje, Mutane Sun Kewaye Motarsa
- Masu zanga-zanga sun kewaye motar shugaban INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan, iyayin ziyararsa a Landan ranar Alhamis, 12 ga Nuwamba, 2026
- Masu zanga-zangar sun bukaci ya yi murabus bisa zargin samun kura-kurai a kundin rajistar masu zaɓe na farko
- Zarge-zargen sun haɗa da maimaita sunayen masu zaɓe, amfani da hotunan da aka samar da fasahar AI da kuma ƙirƙirar rumfunan zaɓe na bogi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
London, England - Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya hadu da fushin masu zanga-zanga yayin ziyarar da ya kai birnin Landan na ƙasar Birtaniya a ranar Alhamis, 12 ga Nuwamba, 2026.
Masu zanga-zangar sun kewaye motar da ke ɗauke da shi a wajen cibiyar Chatham House, inda suka riƙa ihu tare da bayyana zarge-zarge kan yadda suke ganin ana gudanar da wasu ayyukan hukumar.

Kara karanta wannan
IReV: INEC ta ɗauki darasi, ta magance abin da ake tsoron zai iya faruwa a zaben 2027

Source: Facebook
Leadership ta ruwaito cewa masu zanga-zangar ’yan Najeriya ne da ke zaune a ƙasashen waje, waɗanda ke fafutukar ganin an samu gaskiya da sahihanci a harkokin zaɓe a ƙasar.
A yayin zanga-zangar, sun yi kira ga Amupitan da ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban INEC, bisa zargin samun kura-kurai a kundin rajistar masu zaɓe na farko da hukumar ta fitar.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun kai ga bayyana INEC a matsayin “ƙungiyar masu aikata laifuffuka”, yayin da suke nuna rashin amincewarsu da yadda hukumar ke tafiyar da wasu al’amuran da suka shafi zaɓe.
Zarge-zargen da suke yi wa INEC
Daga cikin koke-koken da masu zanga-zangar suka gabatar akwai zargin cewa kundin rajistar masu zaɓe na farko ya ƙunshi sunayen da aka maimaita, lamarin da suka nuna a matsayin abin damuwa game da sahihancin bayanan masu zaɓe.
Sun kuma yi zargin cewa an yi amfani da hotunan da aka samar ta hanyar fasahar basirar na’ura (AI) a cikin bayanan rajistar.

Kara karanta wannan
Shugaban INEC ya tafi ƙasar waje, ya faɗa wa duniya matakin da za su ɗauka kan takarar Atiku a 2027
Bugu da ƙari, sun yi iƙirarin cewa akwai rumfunan zaɓe na bogi a cikin bayanan da suka shafi tsarin zaɓe.
Masu zanga-zangar sun danganta waɗannan zarge-zargen da bukatarsu ta ganin an ɗauki mataki kan jagorancin hukumar. Sun kuma buƙaci shugaban INEC ya sauka daga mukaminsa.
Zanga-zangar ta gudana ne a lokacin da Amupitan ya kai ziyara Chatham House, inda aka shirya zai halarci wata tattaunawa kan tsarin zaɓe a Najeriya.
A yayin da shugaban INEC ya je wajen taron, masu zanga-zangar sun yi amfani da damar ziyarar wajen bayyana korafe-korafensu da kuma neman ya ɗauki alhakin zarge-zargen da suka shafi rajistar masu zaɓe.
Amupitan zai karbi mukami bayan INEC?
Kun ji cewa shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC, Joash Amupitan, ya ce a zai karɓi wani mukamin siyasa ko diflomasiyya ba bayan kammala aikinsa.
Ya ƙara da cewa aikin INEC nauyi ne na ƙasa baki ɗaya, kuma ya kamata wanda ya yi hidimar jama'a tsawon lokaci ya samu damar kula da kansa.
Asali: Legit.ng