CBN Ya Amince Wani Kamfanin Duniya Ya Bude Sabon Banki a Najeriya, An Raɗa Masa Suna
- Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ba katafaren kamfanin harkokin kuɗi na duniya, JPMorgan, amincewar farko ta kafa bankin kasuwanci a Najeriya
- Sabon bankin zai taimaka wajen ƙarfafa kasuwannin kuɗi da kuma jawo ƙarin zuba jari daga ƙasashen waje
- CBN ya kuma amince da naɗin Adedapo Adedayo Olagunju a matsayin manajan daraktan bankin da aka tsara kafawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ba katafaren kamfanin harkokin kuɗi na duniya, JPMorgan, amincewar farko ta kafa bankin kasuwanci a Najeriya.
Matakin bankin CBN na iya taimakawa wajen ƙarfafa kasuwannin kuɗi na ƙasar da kuma jawo ƙarin jarin ƙasashen waje.

Source: Twitter
Sunan sabon bankin da za a kafa
The Nation ta ruwaito cewa bankin da aka tsara kafawa, wanda za a kira da suna, JPMorgan Merchant Bank Nigeria Limited, ya samu amincewar farko (Approval-in-Principle) daga CBN.

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: An gano masu shirya kai farmaki kan matasan da za su y aikin zaɓen 2027
Sai dai har yanzu dole ne ya cika wasu ƙa’idojin da hukumomin kula da harkokin kuɗi suka gindaya tare da samun lasisin gudanar da ayyuka na ƙarshe kafin ya fara kasuwanci.
Michael Akuka, daraktan sashen yaɗa labarai na kamfanoni da hulɗa da masu zuba jari na CBN, ne ya sanar da amincewar a ranar Juma’a.
Ya ce hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da aiwatar da sauye-sauye domin ƙarfafa fannin harkokin kuɗi, ƙara amincewar kasuwa da kuma zurfafa alaƙar Najeriya da kasuwannin jarin duniya.
“An bada izini ne bayan nasarar aiwatar da shirin ƙara fadada jarin bankunan Najeriya, wanda ya ƙarfafa tsarin bankunan ƙasar da kuma ƙarfin gudanar da ayyukansu,” in ji sanarwar.
Manufofin sauye-sauyen CBN
Da yake magana kan manyan manufofin sauye-sauyen da CBN ke aiwatarwa, gwamnan bankin, Olayemi Cardoso, ya ce bankin ya ƙuduri aniyar gina ingantaccen tsarin kuɗi mai zaman lafiya da gasa.
“Manufarmu ita ce gina tsarin kuɗi mai tsafta, mai gasa kuma mai alaƙa da ƙasashen duniya, wanda mutane za su amince da shi, kuma zai iya tallafa wa zuba jari da bunƙasar tattalin arziƙi yadda ya kamata,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa CBN na farin ciki da yadda cibiyoyin kuɗi na ƙasashen duniya ke ƙara nuna sha’awar zuba jari a Najeriya.
Ya ce bankin zai ci gaba da aiwatar da sauye-sauye domin ƙarfafa amincin kasuwannin kuɗin ƙasar, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Naɗa shugabannin bankin
CBN ya kuma amince da naɗin Mista Adedapo Adedayo Olagunju a matsayin shugaban bankin kasuwancin (MD) da ake shirin kafawa.
Haka kuma, bankin ya amince da naɗin Latter Kevin George, Nzelu Chinedum Izunwanne da Syed Gabriel Murtaza a matsayin daraktoci.

Source: Facebook
An kuma amince da Alade Sarah Omotunde, Ajayi Olukonyinsola da Adetu Seni a matsayin daraktoci masu zaman kansu waɗanda ba sa gudanar da ayyukan yau da kullum.
Bankin da aka tsara kafawa zai fara gudanar da ayyukansa ne kawai bayan CBN ya ba shi cikakken lasisin aiki.
CBN ya yi gargadi kan Naira
Kun ji cewa CBN ya bukaci ’yan kasuwa da mazauna Kano su rika kula da takardun Naira, tare da nuna masu illar rashin kula da takardun kudin Najeriya.
Bankin ya bayyana cewa rashin kula da takardun kudin na jawo lalacewarsu, wanda ke tilasta wa gwamnati kashe makudan kudi wajen sauya takardun da suka lalace ko suka baci.
Asali: Legit.ng
