Bayan Maganar Tashin Kiyama, Sabon Wata Ya Fito a Duniya

Bayan Maganar Tashin Kiyama, Sabon Wata Ya Fito a Duniya

  • Rahoto ya nuna cewa wani ƙaramin wata mai suna Asteroid 2026 QQ8 ya shiga sararin da ƙarfin sama tare da jan hankalin duniya
  • Masana ilmin taurari sun ce wannan sabon watan zai zagaye duniya sau ɗaya da rabi kafin ya rage tasiri a shekarar 2027
  • Watan mai faɗin kimanin mita biyu ba ya barazana ga duniya, kuma ba shi ne karon farko da aka samu irin shi a sararin samaniya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Duniya ta samu wani sabon ƙaramin wata da ke zagayawa a kusa da ita bayan ya shiga ƙarƙashin tasirin sararin samaniya.

Tauraron, wanda aka sanya wa suna Asteroid 2026 QQ8, ya fara zagaya wa ne a watan Afrilun 2026, inda zai ci gaba da kewaya duniya na ɗan lokaci kafin ya fice a shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Shugaban INEC na shirin murabus daga muƙaminsa kafin zaɓen 2027? Gaskiya ta fito

Wata a duniyar da muke ciki
Wata a sararin samaniya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jaridar The Independent ta rahoto cewa wani masani kan ilmin taurari ɗan ƙasar Hungary, Kriztián Sárneczky, ne ya fara gano wannan tauraro.

Yadda watan ke zagaya duniya

Rahoton ya bayyana cewa Sárneczky, wanda ya shahara wajen gano ƙananan duwatsun sararin samaniya, ya fara ganin tauraron ne a watan Agusta amma Cibiyar Ƙananan Taurarin Duniya ta Hukumar Ƙasa da Ƙasa ta Ilmin Taurari (IAU) ce ta fitar da rahotonsa a baya-bayan nan.

Binciken hanyarsa ya nuna cewa Asteroid 2026 QQ8 zai ɗauki kwanaki 359 wajen zagaya rana, kuma yana kusantar duniya kusan sau ɗaya a cikin shekaru 10.

Ana sa ran zai zagaye duniya sau ɗaya da rabi kafin ya fita daga ƙarƙashin sararin samaniya mai jan hankali a shekarar 2027.

Watan ba ya barazana ga duniya

Masana sun kiyasta cewa mafi kusancin da wannan watan zai yi da duniya yayin zagayawarsa shi ne kilomita 568,000.

Kara karanta wannan

Faɗa ya kaure tsakanin Netanyahu da wanda ya ba shi wuta a zaɓe kan yaƙin Iran

Yahoo News ta wallafa cewa wannan tazara ta kai kusan ninki ɗaya da rabi na matsakaicin nisan da ke tsakanin duniya da wata.

Tauraron yana da faɗin kimanin mita biyu, kuma masana sun ce ba ya da haɗari ga duniya. Sun bayyana cewa da a ce zai yi karo kai tsaye da duniya, da alama yanayin sararin samaniya zai tarwatsa shi kafin ya isa doron ƙasa.

Masana sun bayyana cewa ba sabon abu ba ne a samu ƙananan duwatsun sararin samaniya suna zagaya duniya na ɗan lokaci.

Jinjirin wata a sama
Lokacin da jinjirin wata ya fito. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Wani bincike da aka gudanar a shekarar da ta gabata ya nuna cewa duniya na iya samun har ƙananan watanni shida a lokaci guda, waɗanda ba sa dawwama.

Magana kan tashin kiyama

A wani labarin, kun ji cewa malamin addinin Musulunci, Sheikh Muhammad bin Salih Al-Munajjid, ya bayyana cewa babu wani ingantaccen dalili da ya tabbatar da cewa Alƙiyama za ta tashi a shekarar 2026.

Malamin ya ce alamomin tashin Alƙiyama sun kasu gida biyu, wato ƙanana da manya, inda ya bayyana cewa wasu daga cikin ƙananan alamomin sun riga sun bayyana.

Ya kuma bayyana cewa akwai manyan alamomi guda 10 da za su bayyana a kusa da tashin Alƙiyama, kuma za su biyo juna cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng