Hankali Ya Kwanta: An Bayyana Dalilin da Ya Sa Wasu ba Su Samu Saƙon Tallafin N50,000 ba
- Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilin da ya sa wasu ba su samu saƙon tallafin N50,000 ba har kawo yanzu
- Gwamnati ta ce ana tura wa mutane tallafin N50,000 ne a mataki mataki, kuma ana tura saƙonnin sanarwa ga waɗanda suka cancanta rukuni-rukuni
- Rashin samun saƙon waya ba yana nufin an cire mutum daga cikin waɗanda za su amfana da shirin NERSI ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilin da ya sa wasu ’yan Najeriya ba su samu saƙon waya da ke sanar da su cewa suna cikin wadanda za a bai wa tallafin N50,000 ba.
Hakan na zuwa ne bayan wasu mutane sun fara korafin kana rashin samun sakonnin tallafi karkashin shirin National Emergency Relief and Stabilisation Intervention (NERSI).

Source: Facebook
A bayanin da ta wallafa a shafin yanar gizo na NERSI, gwamnati ta ce ana tura wa mutane tallafin kudin ne a matakai daban-daban kuma an tura masu saƙon waya rukuni rukuni.

Kara karanta wannan
Kare ya haddasa babbar matsala da ake zargin ta jawo kashe wani bawan Allah a Kano
Dalilin jinkirin tura tallafin N50,000
Gwamnatin ta ce jinkirin samun saƙon sanarwa ba lallai ne ya nuna cewa mutum ba ya daga cikin waɗanda za su amfana da shirin.
A cewar bayanan tambayoyi da amsoshi kan shirin, an ce masu gudanar da biyan kuɗin na tuntuɓar waɗanda suka cancanta a rukuni-rukuni. Hakan na nufin wasu waɗanda aka zaɓa na iya samun saƙonsu ne bayan wasu.
“Ana biyan kuɗin ne a matakai daban-daban. Masu tura kuɗin na tuntuɓar waɗanda suka cancanta rukuni-rukuni, saboda haka mai yiwuwa saƙon SMS ɗinku bai iso ba tukuna,” in ji sanarwar.
Sai dai gwamnatin ta bayyana cewa ba kowa ne za a zaɓa a wannan matakin ba, domin an tsara shirin ne domin tallafa wa wani adadi na talakawa a kowane rukuni.
Yadda za a tantance matsayi
Gwamnatin ta shawarci ’yan Najeriya da ke son tabbatar da matsayinsu da su danna lambar USSD ta kamfanin da ke kula da biyan kuɗinsu, sannan su zaɓi hanyar tantance cancantarsu.

Kara karanta wannan
Moniepoint ya fitar da hanya mai sauki ta duba waɗanda za su samu tallafin N50,000
Ta ce waɗanda ba sa cikin jerin waɗanda za su amfana za su samu saƙon sanarwa mai cewa: “A halin yanzu ba a zaɓe ku cikin waɗanda za su samu wannan tallafin ba.”

Source: Getty Images
Yadda shirin NERSI ke aiki
Shirin NERSI na ƙarƙashin Ma’aikatar Jinƙai da Rage Talauci ta Tarayya, kuma an tsara shi ne domin taimaka wa gidaje su iya fuskantar hauhawar tsadar rayuwa.
A ƙarƙashin shirin, waɗanda aka zaɓa suna samun tallafin N50,000 kowannensu ta asusun kamfanonin hada-hadar kudi guda biyar da gwamnati ta amince da su.
Yadda za ku duba kudin a Moniepoint
Kun ji cewa kamfanin hada-hadar kudi na Moniepoint ya yi bayani kan yadda mutane za su duba cancantarsu ta karbar tallafin N50,000 daga gwamnatin tarayya.
Waɗanda aka tabbatar sun cancanta za su iya karɓar kuɗin kai tsaye a asusun Moniepoint ba tare da an daukar masu ko kwandala ba.
Asali: Legit.ng