Babbar Kotu Ta Karbi Shaidu kan Wadanda Ake Zargi da Yunkurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki
- Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta amince da wasu shaidu da gwamnatin tarayya ta gabatar kan mutum shida da ake zargi da hannu a kitsa juyin mulki
- Daga cikin shaidun akwai bayanan da wadanda ake zargin suka bayar a gaban kwamitin bincike na musamman da rundunar soji
- Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta yi watsi da ikirarin cewa an tilasta wa wadanda ake zargin yin furuci, inda ta ce ba su gabatar da hujjar da ta tabbatar da hakan ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta amince da shaidun da gwamnatin tarayya ta gabatar kan mutum shida da ake zargi da hannu a wani yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta hanyar juyin mulki.
Daga cikin shaidun da kotun ta amince da su akwai bayanan da wadanda ake tuhumar suka bayar a gaban kwamitin bincike na musamman da kuma jami’an rundunar ’yan sandan soji.

Source: Getty Images
Vanguard ta ruwaito cewa mutanen da ake shari’a da su kan zargin yunkurin juyin mulkin sun hada da Manjo Janar Mohammed Ibrahim Gana (mai ritaya) da Kyaftin din Rundunar Sojin Ruwa Erasmus Ochegobia Victor.
Sauran su ne Zekeri Umoru, Bukar Kashim Goni da Abdulkadir Sani da sufeto Ahmed Ibrahim mai aiki a rundunar ’yan sandan Najeriya.
Ana tuhumar mutanen ne da laifuka 13 karkashin lambar shari’a FHC/ABJ/CR/206/2026.
Kotu ta fara karbar shaidu
Lauyoyin wadanda ake tuhuma sun kalubalanci amincewa da bayanan da wadanda ake zargin suka bayar, bisa hujjar cewa an tilasta musu yin hakan ta hanyar barazana da matsin lamba.
Lauyoyin sun kuma yi ikirarin cewa an hana wadanda ake zargin damar samun wakilcin lauya yayin yi musu tambayoyi, tare da jaddada cewa akwai sabanin da ke tsakanin bidiyon da aka dauka da kuma rubutattun bayanan da suka bayar.
Sai dai masu gabatar da kara sun bukaci kotun ta yi watsi da korafe-korafen.

Kara karanta wannan
Ciyaman ya sha da ƙyar da miyagun yan daba suka farmaki wurin zaɓen fitar da gwanin APC
Duk da haka, Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta bayar da umarnin gudanar da shari’a ta musamman a cikin shari’ar domin tantance ko wadanda ake tuhuma sun bayar da bayanan nasu da radin kansu.
Lamarin ya taso ne yayin da shaida na hudu a bangaren masu gabatar da kara ke bayar da shaida.
Matsayar da kotun tarayya ta dauka
A hukuncin da ta yanke a ranar Alhamis, Mai shari’a Abdulmalik ta ce wadanda ake tuhuma sun gaza tabbatar da zargin cewa an tilasta musu yin furucin amsa laifi.
Kotun ta bayyana ikirarin cewa sun yi furucin ne a karkashin matsin lamba a matsayin wani abu da suka kirkira daga baya, sannan ta yi watsi da zargin azabtar da su.

Source: Twitter
Daga nan ne ta amince da rubutattun bayanan wadanda ake tuhuma da kuma bidiyon da aka dauka a matsayin wani bangare na shaidun da za a yi amfani da su a shari’ar.
Mai shari’a Abdulmalik ta sanya ranakun 7 da 10 ga watan Disamba, 2026 domin ci gaba da sauraron karar.
Yadda aka raba kudin juyin mulki
Kun ji cewa masu bincike sun zargi tsohon gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva, da bayar da gudunmuwar kuɗi domin yunkurin juyin mulkin 2025 ta hannun wani kamfani.
Rahotanni sun ce an raba sama da N700m ga jami'an soja, malamai da wasu fararen hula bisa umarnin Kanal Mohammed Ma'aji
Asali: Legit.ng
