Alherin da Soja Ya Samu bayan ƙin Karɓar Cin Hancin N500,000 daga Ɗan Bindiga
- Wani soja mai suna Utim Terwase ya ƙi karɓar cin hancin N500,000 daga hannun wani da ake zargi da yin garkuwa da mutane a jihar Plateau
- Rundunar Operation Enduring Peace ta ba sojan kyautar N500,000 saboda nuna gaskiya, biyayya da ƙin karɓar kuɗin rashawa
- Kwamandan rundunar ya yabawa sojan tare da kira ga sauran jami’an tsaro da su yi koyi da halayensa na gaskiya da riƙon amana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Jos, Plateau - Rundunar sojojin da ke gudanar da aikin Operation Enduring Peace a jihar Plateau ta ba wani soja kyautar N500,000 bayan ya ƙi karɓar cin hanci makamancin wannan kuɗi daga hannun wani da ake zargi da yin garkuwa da mutane.
Sojan mai suna Utim Terwase ya samu wannan kyauta ne saboda ƙin sakin wanda ake zargin bayan ya yi ƙoƙarin tserewa daga hannun jami’an tsaro.

Source: UGC
Mai magana da yawun rundunar haɗin gwiwar sojojin a jihar Plateau, Kyaftin Chinonso Oteh, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Jos, cewar Punch.
Yadda sojan ya ƙi karɓar cin hancin N500,000
Oteh ya bayyana cewa Terwase ya kama wanda ake zargin ne bayan ya yi ƙoƙarin tserewa, amma mutumin ya yi masa tayin N500,000 domin ya sake shi.
Sai dai sojan ya ƙi amincewa da tayin, inda ya miƙa wanda ake zargin ga hukumomin da suka dace domin gudanar da bincike da sauran matakan shari’a.
Rundunar sojoji ta ba shi kyautar N500,000
Domin nuna godiya ga gaskiyarsa, ladabi da jajircewa wajen gudanar da aikinsa, kwamandan Operation Enduring Peace, Manjo Janar Maxwell Dangana, ya ba Terwase kyautar N500,000.
Wannan kuɗi ya yi daidai da adadin kuɗin da sojan ya ƙi karɓa a matsayin cin hanci daga wanda ake zargin.
Oteh ya nakalto Dangana, wanda ya yi magana ta bakin kwamandan Sector 6 na rundunar, Kanal Philimon Malgwi, yana cewa halin sojan ya nuna kyawawan ƙa'idojin aikin soja da biyayya ga ƙasa.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: Mai garkuwa da mutane ya shiga hannu yana kokarin karbar kudin fansa
Ya ce maimakon ya ci amanar aikinsa domin samun abin duniya, Terwase ya tsaya kan gaskiya, riƙon amana da gudanar da aikinsa yadda ya kamata.

Source: Original
An bukaci sauran sojoji su yi koyi da shi
Sanarwar ta bayyana cewa Operation Enduring Peace ta yaba wa Terwase tare da ƙarfafa sauran jami’an rundunar da su yi koyi da irin wannan hali na gari.
Ta ƙara da cewa wannan kyauta na nuna aniyar rundunar wajen inganta gaskiya, riƙon amana da ƙwarewa a yayin gudanar da ayyukan da kundin tsarin mulki ya ɗora mata.
Rundunar sojojin ta ce wannan mataki ya aika da saƙo mai ƙarfi ga jami’anta da sauran ’yan Najeriya cewa gaskiya da riƙon amana muhimman halaye ne da ya kamata a yaba musu.
Ta kuma bayyana cewa a lokacin da cin hanci da rashawa ke ci gaba da rage amincewar jama’a da hukumomi, matakin Terwase ya nuna cewa mutum na iya zaɓar gaskiya ko da kuwa an jarabce shi, cewar Vanguard.
Sanarwar ta ce:
“Sojan da ya ƙi karɓar N500,000 na kuɗin haram, ya samu N500,000 na girmamawa. Haƙiƙa, gaskiya tana da lada.”

Kara karanta wannan
Aminu Abdulsalam ya bayyana mutanen da yake zargi da yunkurin hana shi takara a Kano
An yanke wa soja hukuncin kisa
A wani labarin, an ji cewa kotun sojoji a Jos ta yanke wa soja hukuncin rataya bayan kama shi da laifin kashe mai Keke Napep a jihar Bauchi.
Rahotanni sun nuna cewa sojan ya hada baki da abokinsa, suka jawo marigayin cikin gida, suka buge shi, sannan suka shake shi.
Alkalin kotun ya nuna damuwa kan yadda soja ya canza daga mai kare jama’a zuwa kisa yana mai kiran aikinsa abin kunya ga rundunar.
Asali: Legit.ng
