MURIC za Ta Yi Zanga Zanga kan Hana Mata Sa Hijabi a Makarantar Lauyoyi

MURIC za Ta Yi Zanga Zanga kan Hana Mata Sa Hijabi a Makarantar Lauyoyi

  • Kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC ta bukaci a dakatar da jarabawar dukkan cibiyoyin makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya
  • A bayanin da ta yi, kungiyar ta yi zargin cewa an ci zarafin dalibai mata Musulmi masu hijabi tare da hana wasu shiga zauren jarabawa
  • MURIC ta yi barazanar shirya zanga-zangar lumana a dukkan cibiyoyin makarantar idan ba a biya bukatunta ba game da mata Musulmi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC ta bukaci a dakatar da jarabawar karshe da daliban makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya ke yi, sakamakon zargin hana dalibai mata Musulmi masu hijabi shiga dakunan jarabawa.

Kungiyar ta kuma bukaci gudanar da bincike kan lamarin, wanda ta ce ya faru a ranar Asabar, 31 ga watan Oktoba, 2026, yayin jarabawar karshe ga daliban da ke shirin shiga aikin lauya.

Kara karanta wannan

Gwamna Bala ya yi ta'aziyyar babban dan siyasar da ya rasu a Bauchi

Ishaq Akintola a wajen taro
Shugaban MURIC, Ishaq Akintola. Hoto: MURIC
Source: Twitter

Daily Trust ta rahoto cewa shugaban MURIC Farfesa Ishaq Akintola ya yi barazanar shirya zanga-zangar lumana a dukkan cibiyoyin makarantar idan ba a dauki mataki ba.

Batun hana masu hijabi jarabawa

Farfesa Akintola ya ce kungiyar ta samu rahotannin cewa an hana wasu dalibai mata masu hijabi shiga dakunan jarabawa a sassa daban-daban na kasar saboda sanya hijabin.

Ya yi zargin cewa an tilasta wa wasu daga cikinsu tsayawa a waje na kusan awa guda kafin daga bisani aka ba su damar shiga bayan sun cire hijabinsu.

A cewarsa, kungiyar ta samu kiran waya da sakonnin damuwa daga daliban da abin ya shafa, iyayensu da sauran Musulmi a lokacin da lamarin ke faruwa.

Akintola ya bayyana cewa MURIC ta yi Allah wadai da abin da ta kira cin zarafi da tauye hakkin dalibai mata Musulmi na neman ilimi da ci gaba a sana'arsu.

Kara karanta wannan

Babbar matsala ta tunkaro Tinubu, rikicin tikitin sanatan APC zai iya taɓa ƙuri'unsa

MURIC ta kare saka hijabi

Kungiyar ta yi nuni da sashe na 38(1) da (2) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999, wanda ya ba kowane mutum damar yin addininsa da bayyana akidarsa.

Ta kuma ambaci hukuncin Kotun Koli na shekarar 2022 a shari'ar gwamnatin jihar Legas da Asiyat Abdulkareem, inda ta ce kotun ta tabbatar da cewa hana ko takaita sanya hijabi na iya zama nuna wariya.

MURIC ta kara da cewa abin da ake zargin ya faru ya saba wa sashe na 42 na kundin tsarin mulki, wanda ya haramta nuna wariya ga kowane mutum.

Haka kuma, kungiyar ta yi nuni da sashe na 34(1)(a), wanda ya tanadi kare mutuncin dan Adam tare da hana azabtarwa ko wulakanta mutum.

Shuugaban kungiyar MURIC
Shugaban kungiyar MURIC yana wa'azi. Hoto: MURIC
Source: Twitter

MURIC ta yi barazanar zanga-zanga

MURIC ta bukaci a dakatar da jarabawar a dukkan cibiyoyi a Najeriya har sai an gudanar da bincike kan zargin da aka gabatar.

Leadership ta rahoto cewa ta kuma bukaci a dauki matakan da za su hana sake faruwar irin wannan lamari ga dalibai mata Musulmi masu hijabi.

Kara karanta wannan

Akwai babban dalili: Makiyaya sun faɗi musabbabin shirin goyon bayan Tinubu

Kungiyar ta yi gargadin cewa idan ba a biya bukatunta ba, za ta hada kai da iyaye, matasan Musulmi da sauran masu ruwa da tsaki domin gudanar da zanga-zangar lumana a cibiyoyin makarantar a fadin kasar.

An ceto malaman Musulunci

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar ’yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da ceto malaman addinin Musulunci guda uku daga cikin shida da aka sace a ranar 12 ga watan Satumba.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Muhammad Bello, ne ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa da manema labarai a Gusau ranar Juma’a.

Ya ce an samu nasarar ceton malaman ne ta hanyar hadin gwiwar hukumomin tsaro daban-daban, ciki har da ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA).

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng