'Yan Bindiga: An Tura Sabuwar Bataliyar Sojoji Jihar Kano

'Yan Bindiga: An Tura Sabuwar Bataliyar Sojoji Jihar Kano

  • Rundunar sojin Najeriya ta tura bataliya da rundunar manyan makamai zuwa jihar Kano domin ƙarfafa tsaro da magance barazanar tsaro
  • Kwamandan rundunar soji ta 1, Manjo Janar Abubakar Muhammad Wase, ya ce sojojin na buƙatar jajircewa, juriya da isasshen tallafi
  • Wase ya buƙaci al’ummomin Dambatta da Tudun Wada su haɗa kai da sojoji domin inganta tsaro, yayin da ake ci gaba da fuskantar matsalar garkuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Rundunar sojin Najeriya ta tura bataliya da runduna ta musamman zuwa jihar Kano a wani mataki na ƙarfafa tsaro da inganta yadda sojoji za su mayar da martani kan sababbin barazanar tsaro.

Kwamandan rundunar soji ta 1 ta Najeriya kuma kwamandan ɓangare na 1 na rundunar haɗin gwiwa ta Operation Fansan Yamma, Manjo Janar Abubakar Muhammad Wase ne ya sanar da haka.

Kara karanta wannan

An tura fitacciyar fim kurkuku kan zargin fitar da hoton tsiraici

Sojojin Najeriya a bakin aiki
Wasu dakarun Najeriya a cikin daji. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Wase ya bayyana hakan ne yayin ziyarar tantance ayyukan sojoji a bataliya ta 24 da ke Tudun Wada da kuma rundunar manyan makamai ta 311 da ke Dambatta, jihar Kano, tsakanin 28 zuwa 29 ga Oktoba, 2026.

An kara rundunonin tsaro a Kano

A cewar wata sanarwa da mataimakin daraktan hulɗa da jama’a na rundunar soji ta 1, Kanal Abubakar Abdullahi, ya fitar ranar Alhamis, Wase ya tabbatar wa sojojin cewa rundunar tana aiki kafada da kafada da gwamnatin jihar Kano.

Ya ce:

“Kasancewar waɗannan sababbin rundunoni ne da aka kafa kwanan nan, suna buƙatar haɗin kai, juriya da jajircewa domin cimma manufofin da aka kafa su.”

Wase ya ƙara da cewa kula da walwalar sojoji da samar musu da kayan aiki da sauran tallafin gudanarwa na daga cikin abubuwan da rundunar ta ba muhimmanci.

Ya bayyana cewa rundunar za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da cewa sababbin rundunonin sun samu ƙarfin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Iran: An sauke babban sojan da ke yi wa amurka tsare tsaren kai farmaki

Kwamandan ya nemi haɗin kai

PR Nigeria ta wallafa cewa a yayin ziyarar, Wase ya samu rakiyar kwamandan rundunar soji ta 3, Birgediya Janar Saka Jimoh.

Sun kuma gana da jami’an ƙananan hukumomin Dambatta da Tudun Wada domin tattauna batutuwan da suka shafi tsaro da ayyukan sabbin rundunonin.

Kwamandan ya buƙaci al’ummomin yankunan da su ba sojoji haɗin kai tare da tallafa wa rundunonin domin inganta tsaro a faɗin jihar Kano.

Taswirar jihar Kano
Taswirar jihar Kano a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Ya jaddada cewa haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen samar da yanayin da mazauna yankunan za su rayu cikin kwanciyar hankali.

An sace mai juna biyu

A wani labarin, kun ji cewa wata mata mai juna biyu mai suna Jamila da ’yan bindiga suka sace a gidanta da ke Alrahus Estate, Millennium City, jihar Kaduna, ta shafe mako uku a hannun masu garkuwa da mutane.

An sace Jamila ne ranar 6 ga Oktoba tare da Abubakar Zakka, matarsa da jaririyarsu mai wata shida, lokacin da ’yan bindigar suka kai hari gidansu da ke ƙaramar hukumar Chikun.

Wata majiya da ke da masaniya kan tattaunawar neman sakin waɗanda aka sace ta ce masu garkuwar sun kira ranar Talata, inda Jamila ta bayyana cewa ta yi ɓari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng