Gwamnatin Tinubu na Shirin Sanya INEC Dage Zaben 2027? An Ji Yadda Zancen Yake

Gwamnatin Tinubu na Shirin Sanya INEC Dage Zaben 2027? An Ji Yadda Zancen Yake

  • Gwamnatin Tarayya ta yi magana kan zargin shirin sauya ranar zaɓen shekarar 2027 da ake tunkara nan da 'yan watanni
  • ADC ta yi zargin cewa ana shirin gayyatar shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, zuwa fadar shugaban ƙasa domin matsa masa lamba ya sauya jadawalin zaɓe
  • Jam’iyyar ADC ta buƙaci Amupitan ya ƙi duk wani umarni na sauya ranar zaɓe tare da bayyana wa jama’a duk wata matsin lamba da aka yi masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta yi magana kan zargin cewa gwamnatin tarayya na shirin sauya ranar zaben 2027.

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa labarin ƙarya ne zargin cewa Gwamnatin Tarayya na shirin sauya ranar zaɓen shugaban ƙasa da aka tsara gudanarwa a ranar 16 ga Janairu.

An karyata batun shirin sauya ranar zaben 2027
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: @inecnigeria, @aonanuga1956
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan.

Kara karanta wannan

Ana batun shirin dage zaben 2027, majalisa ta gayyaci shugaban INEC

Tun da farko, Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar ADC ya yi zargin cewa akwai wani shiri na matsa wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) lamba domin sauya ranar zaɓen.

Jam’iyyar ta kuma gargaɗi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kada ya yi ƙoƙarin kauce wa hukuncin da masu zaɓe za su yanke ta hanyar jefa ƙuri’unsu.

Gwamnatin tarayya ta musanta zargin

Da yake mayar da martani kan zargin, Mohammed Idris, ya ce gwamnati ba ta da masaniyar wani shiri na sauya ko ɗage ranar zaɓe.

Ministan ya bayyana cewa babu wani shiri da Gwamnatin Tarayya ke yi na sauya ranar zaɓen, yana mai cewa zargin ba shi da tushe.

"Gwamnatin Tarayya ba ta shirin sauya ranar zaɓe ko ɗage wani zaɓe. Babu irin wannan shiri, kuma gwamnati ba ta da masaniya a kansa. A wurinmu, wannan labarin ƙarya ne kawai.” In ji shi.

Kara karanta wannan

To fa: ADC ta fallasa makarkashiyar da ake shiryawa kan zaben 2027, ta ja kunnen Tinubu

ADC ta yi zargin matsa wa INEC lamba

Sai dai, kwamitin ADC ya ce ya samu bayanan da ke nuna cewa ana shirin gayyatar shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, zuwa fadar shugaban ƙasa domin ba shi umarnin sauya jadawalin zaɓe.

A cewar kwamitin yaƙin neman zaɓen, ana zargin shirin ne yayin da kwanaki 80 kacal suka rage kafin gudanar da zaɓen.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Dabarun Yaƙin Neman Zaɓen ADC, Phrank Shaibu, ya fitar, jam’iyyar ta buƙaci Tinubu da ya yi watsi da duk wani shiri makamancin haka.

Ta kuma buƙaci Amupitan da ya ƙi duk wani umarni na sauya ranar zaɓe, tare da bayyana wa jama’a nan take idan wani ya yi ƙoƙarin matsa masa lamba.

Gwamnatin tarayya ta musanta shirin dage zaben 2027
Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris Hoto: @HMIdris
Source: Twitter

Majalisa ta gayyaci shugaban INEC

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar wakilai ta gayyaci shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan.

Majalisar wakilan ta gayyaci Amupitan ne domin ya yi bayani kan shirye-shiryen hukumar na gudanar da babban zaɓen​ 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng