Shiri Ya Yi Nisa: An Fadi Lokacin Samar da 'Yan Sandan Jihohi a Najeriya
- Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya ce shirin kafa rundunar ’yan sandan jihohi a Najeriya zai kammala kafin ko zuwa watan Disamba na 2026
- Ya bayyana cewa aƙalla majalisun dokokin jihohi 30 sun amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki na 2026 da zai ba da damar kafa rundunar ’yan sandan jihohi
- Bamidele ya ce mataki na gaba shi ne Majalisar Tarayya ta tattara rahotannin jihohin, ta amince da kudirin sannan ta miƙa shi ga Shugaban Ƙasa domin sanya hannu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya bayyana cewa shirin kafa rundunar ’yan sandan jihohi a Najeriya zai kammala kafin ko zuwa watan Disamba na shekarar 2026.
Bamidele ya ce batun kafa rundunar ya samu gagarumin ci gaba bayan aƙalla majalisun dokokin jihohi 30 sun amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ya shafi kafa ’yan sandan jihohi.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta rahoto cewa Bamidele ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin gabatar da takarda a Cibiyar Nazarin Manufofi da Dabarun Ƙasa (NIPSS) da ke Kuru, jihar Filato.
Jihohi 30 sun amince da kudirin
Bamidele, wanda shi ne mataimakin shugaban kwamitin Majalisar Dattawa kan sake duba kundin tsarin mulkin 1999, ya bayyana cewa kafa ’yan sandan jihohi ya wuce matakin alkawarin siyasa zuwa wani shiri da kundin tsarin mulki zai amince da shi.
Ya yi jawabin ne ga mahalarta kwas ɗin manyan jami’an gudanarwa na 48 (SEC 48), a kan taken inganta inganci da tasirin shugabanci ta hanyar samar da dokoki tun da wuri.
Sanatan ya ce amincewar majalisun jihohi 30 ta cika ƙa’idar kashi biyu bisa uku da sashe na 9(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya tanada domin yin gyara.
Daily Trust ta rahoto ya ce:
“Muna farin cikin sanar da al’ummominmu a faɗin ƙasa cewa batun ’yan sandan jihohi ya wuce zance kawai zuwa ga abin da ya zama gaskiya.

Kara karanta wannan
Yadda 'yan bindiga suka kafa gwamnatinsu, suke karɓar haraji kala 3 a jihohin Arewa 2
“Bisa tanadin sashe na 9(2) na kundin tsarin mulkin 1999, wanda ke buƙatar amincewar aƙalla kashi biyu bisa uku na dukkan majalisun dokokin jihohi, an cika sharuddan kundin tsarin mulki da ake buƙata domin yin wannan gyara.”

Source: Twitter
Matakan da suka rage a kafa 'yan sandan
Shugaban masu rinjayen ya bayyana cewa abin da ya rage yanzu shi ne kammala wasu matakai na majalisa kafin kudirin ya zama doka.
A cewarsa, Majalisar Tarayya za ta tattara rahotannin amincewar da majalisun dokokin jihohi suka bayar, sannan majalisun biyu su amince da kudirin da rinjayen ƙuri’u.
Bayan haka, za a miƙa kudirin ga Shugaban Ƙasa domin sanya hannu, kuma ana sa ran kammala dukkan matakan kafin ko zuwa Disamba na 2026.
An tura karin sojoji zuwa Kano
A wani labarin, kun ji cewa, rundunar sojin Najeriya ta tura sabuwar bataliya da rundunar manyan makamai zuwa jihar Kano domin inganta martaninta kan barazanar tsaro.
Kwamandan rundunar soji ta 1 kuma kwamandan ɓangare na 1 na Operation Fansan Yamma, Manjo Janar Abubakar Sadique Muhammad Wase ne ya sanar da haka.
Wase ya bayyana hakan ne yayin ziyarar tantance ayyukan sojoji a bataliya ta 24 da ke Tudun Wada da rundunar manyan makamai ta 311 da ke Dambatta, tsakanin 28 zuwa 29 ga Oktoba, 2026.
Asali: Legit.ng
