Matar Masussuka Ta Fito da Bayanai kan Yadda aka Harbe Shi har Lahira
- Matar marigayi Sheikh Yahaya Masussuka ta bayyana yadda ’yan bindiga suka harbe mijinta a Dutsin-Ma ta jihar Katsina
- Hajiya Fatima ta ce mijinta ya fita domin zuwa wajen karatu tare da almajiransa kafin ta ji karar harbe-harbe guda huɗu.
- Rundunar ’yan sandan Katsina ta ce har yanzu ba ta tabbatar da ikirarin ƙungiyar Ansaru na cewa ita ce ta kashe malamin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Katsina – Hajiya Fatima Masussuka, matar marigayi Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, ta bayyana yadda wasu ’yan bindiga suka kashe mijinta a karamar hukumar Dutsin-Ma ta jihar Katsina a yammacin ranar Litinin.
Hajiya Fatima ta bayyana hakan ne yayin da take zantawa da ’yan jarida a gidansu ranar Talata, inda ta ce maharan sun kai harin ne jim kadan bayan mijinta ya fita domin zuwa wajen karatu.

Source: Facebook
Yadda aka kashe Yahaya Masussuka
Punch ta wallafa cewa Hajiya Fatima ta ce ta raka mijinta zuwa kofar gidansu yayin da yake shirin tafiya wurin koyar da almajiransa, amma daga baya ta koma cikin gida saboda ya manta da jakarsa.
Amaryar malaman addinin ta ce ba ta dade da komawa cikin gidan ba sai ta ji karar harbe-harbin bindiga guda huɗu.
A cewarta, lokacin da ta fito domin ganin abin da ke faruwa, sai ta tarar an harbi mijinta, har aikin gama ya gama.
Ta bayyana cewa abin ya girgiza ta matuƙa, domin ba ta yi tsammanin hakan zai faru ba.
Irin alakar Fatima da Sheikh Masussuka
Matar malamin ta bayyana marigayin a matsayin miji mai kulawa, tana mai cewa ita ce matarsa ta biyu kuma suna da ’ya mace guda ɗaya.
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa ta ce kafin mijinta ya fita daga gida a ranar da aka kashe shi, sun yi magana kan kadaitar Allah.
Hajiya Fatima ta ce jim kadan bayan fitarsa ne ta ji karar harbe-harbe, sannan daga baya aka sanar da ita cewa an kashe shi.
Kisan Sheikh Yahaya Masussuka ya jawo tambayoyi kan dalilin da ya sa aka kai masa harin, da kuma ko maharan sun san inda zai je ko kuma sun dade suna bibiyarsa.

Source: Facebook
Mutuwar malamin ta kuma sake jawo hankalin jama’a kan saɓanin fahimtar addini da aka danganta da wasu daga cikin koyarwarsa.
Su wa suka kashe Masussuka?
A wani labarin, mun ruwaito cewa ƙungiyar Ansaru ta yi ikirarin kashe Sheikh Yahaya Masussuka a Dutsin-Ma ta jihar Katsina, inda ta zarge shi da kafirci a cikin saƙon murya da aka fitar.
Ansaru na da alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda, kuma ta balle daga Boko Haram a shekarar 2012 bayan samun saɓani da jagorancin ƙungiyar. An danganta ayyukanta da wasu sassan Arewa maso Yammacin Najeriya.
Duk da ikirarin da aka danganta da Ansaru, rundunar ’yan sandan Katsina ta ce ba ta tabbatar da sahihancinsa ba, tana mai cewa ana ci gaba da bincike domin gano waɗanda suka kashe malamin da kuma dalilin aikata laifin.
Asali: Legit.ng

