Shugaba Tinubu Ya ba Tsohon Shugaban DSS, Yusuf Bichi, Gingimemen Mukami
- Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Yusuf Bichi, tsohon Darakta-Janar na DSS, a matsayin shugaban majalisar gudanarwa ta NISS da ke Abuja
- Bichi zai fara wa'adin shekaru huɗu daga ranar 22 ga Oktoba, 2026, bisa dokar kafa cibiyar ta shekarar 2019
- Naɗin nasa ya biyo bayan shawarar Darakta-Janar na DSS na yanzu, Oluwatosin Adeola Ajayi, kuma zai maye gurbin A.A. Gadzama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Yusuf Bichi, tsohon Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), a sabon mukami.
Shugaba Tinubu ya nada Yusuf Bichi a matsayin shugaban majalisar gudanarwa ta Cibiyar Nazarin Tsaro ta Ƙasa (NISS), da ke Lower Usuma Dam, Abuja.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce Lilian Omo-Odigwe, Daraktar Hulɗa da Daidaita Ayyuka ta NISS, ce ta tabbatar da naɗin a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, 22 ga watan Oktoban shekarar 2026.
Sanarwar ta ce naɗin Yusuf Bichi ya biyo bayan shawarar Darakta-Janar na DSS na yanzu, Oluwatosin Adeola Ajayi.
Bichi zai yi wa'adin shekaru 4
A cewar sanarwar, wa'adin farko na Bichi zai kasance na shekaru huɗu, wanda ya fara aiki daga ranar 22 ga Oktoba, 2026.
An bayyana cewa naɗin ya yi daidai da sashe na huɗu na Dokar Kafa Cibiyar Nazarin Tsaro ta Ƙasa ta shekarar 2019.
Bichi zai maye gurbin A.A. Gadzama, OFR, mni, a matsayin shugaban majalisar gudanarwar cibiyar, jaridar Vanguard ta kawo rahoton.
Tsohon shugaban DSS ɗin ya miƙa ragamar shugabancin hukumar ga magajinsa, Oluwatosin Adeola Ajayi, a watan Agustan shekarar 2024.
Tarihin aikin Yusuf Bichi a harkokin tsaro
Sanarwar ta bayyana cewa Yusuf Bichi ya fara aikin gwamnati a sashen tsaro na Ofishin Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano, kafin daga bisani a sauya masa wurin aiki a shekarar 1984.
A cewar NISS, naɗin nasa ya kawo ƙwarewa mai yawa a fannonin tattara bayanan sirri, gudanar da harkokin tsaro, jagorancin ayyukan tsaro da horas da ma'aikata.
Cibiyar ta ce wannan ƙwarewa za ta taimaka wajen gudanar da ayyukan kwamitin da kuma tafiyar da harkokinta.
Naɗin da aka yi wa Yusuf Bichi ya zo ne bayan ya kammala jagorancin DSS a shekarar 2024, inda yanzu zai jagoranci majalisar gudanarwa ta cibiyar da ke da alhakin nazari da horaswa a fannin tsaro.

Source: Twitter
Obasanjo ya soki gwamnatin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya soki manufofin da gwamnatin Bola Tinubu ta aiwatar a fannin tattalin arziki.
Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar, ciki har da rage darajar Naira, sun ƙara tsananta talauci a ƙasar.
Tsohon shugaban kasar ya ce faduwar darajar Naira cikin sauri ta jefa ’yan Najeriya cikin matsin tattalin arziki, tare da taimakawa wajen sanya ƙasar cikin jerin ƙasashen da ke da mafi yawan talakawa a duniya.
Asali: Legit.ng

