Yadda 'yan kungiyar asiri suka makantar da ni saboda na ki shiga kungiyarsu - Matashi

Yadda 'yan kungiyar asiri suka makantar da ni saboda na ki shiga kungiyarsu - Matashi

- Olamilekan Ibidokun matashi mai shekaru 23 ya bayyana yadda 'yan kungiyar asiri suka mayar da shi makaho

- A cewar matashin, sun gayyacesa don ya shiga kungiyarsu amma sai ya nuna baya so kwata-kwata

- Ya ce makami suka soka masa a ido inda a take ya tsiyaye kuma suka dinga kashe kudi a kan idon

Matashi mai shekaru 23 mai suna Olamilekan Ibidokun, ya bada labarin yadda 'yan kungiyar asiri da ke yankin Ketu ta jihar Legas suka mayar da shi makaho bayan ya ki shiga kungiyar.

Kamar yadda yace, lamarin ya faru a watan Disamban 2016 yayin da suka yi wani shagalin biki a yankin Ketu ta jihar Legas, Vanguard ta wallafa.

Ya yi ikirarin cewa, maharan da suka makantar da shi har a halin yanzu suna yawonsu a titi ba tare da an tabbatar da wani lamari adalci a kansu ba.

KU KARANTA: Masu kwasar kananan yara daga Arewa suna siyarwa a Kudu sun gurfana a kotu

Yadda 'yan kungiyar asiri suka makantar da ni saboda na ki shiga kungiyarsu - Matashi
Yadda 'yan kungiyar asiri suka makantar da ni saboda na ki shiga kungiyarsu - Matashi. Hoto daga @Vanguard
Source: Twitter

KU KARANTA: Kotu ta bada umarnin cigaba da kiran Sallah a wani Masallaci da aka hana a kasar Jamus

Ya bayyana tushen halin da yake ciki da ranar da ya hadu da wani Abas, wanda ke zama a Ketu. Ya zargi Abass, wani dan kungiyar Aiye wanda ya bukacesa da ya shiga kungiyar amma ya ki.

Kamar yadda yace: "Shi da sauran 'yan kungiyar sun cigaba da gayyata ta amma na ki shiga kungiyar, hakan yasa suka yanke shawarar ladabtar da ni.

"Na halarci biki a 2016 yayin da aka yi shi a karshen shekara. A nan suka hare ni inda suka lalata min idona. Sun soka min makami a idona wanda haka yasa ya tsiyaye."

"An kwantar da ni a asbitin Bolakunmi da ke Ketu na makonni biyu, daga nan aka mika ni babban asbitin Ikorodu.

"Daga nan an mayar da ni asbitin jami'ar koyarwa na Legas da wasu asibitoci. Daga baya mun gaji sannan muka fawwalawa Allah al'amarinmu," ya kara da cewa.

A wani labari na daban, wata kotun majistare da ke zama a Gombe ta gurfanar da wasu mutum uku a gabanta a kan zarginsu da ake yi da sata tare da siyar da wasu kananan yara 13 a jihar Anambra.

Rundunar 'yan sandan jihar Gombe a ranar 7 ga watan Satumban 2020, ta damke wasu mutum hudu da take zargi da satar kananan yara a arewa suna siyar da su a Kudancin kasar nan.

Mutum ukun da ake zargi sun hada da wata Hauwa Usman mai shekaru 28 da ke zama a Tudun Wada a Gobe, Ali Bala Shaukani mai shekaru 39 da ke zama a Jalingo, jihar Taraba da wata Nkechi Nduliye da ke zama a Nkpor a karamar hukunar Idemili a jihar Anambra.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel