Dan Kungiyar Asiri Ya Dana Wa Kansa Harsashi A Lokacin Da Ya Ke Kokarin Sarrafa Bindiga

Dan Kungiyar Asiri Ya Dana Wa Kansa Harsashi A Lokacin Da Ya Ke Kokarin Sarrafa Bindiga

  • Jami'an hukumar Amotekun na Jihar Ogun sun kama wani Janai Sunday wanda ake zargi dan kungiyar asiri ne
  • An kama Janai ne a cikin wani daji da ke hanyar kauyen Obada-Owode, karamar hukumar Imeko-Afon, Ogun bayan ya harbi kansa a hannu cikin tsautsayi
  • David Akinremi, shugaban Amotekun na Imeko-Afon ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce karar harbin bindigan yasa suka shiga daji suka kamo wanda ake zargin a wurin da suke taro

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani da ake zargin dan kungiyar asiri ne ya harbi kansa a yayin da ya ke kokarin ciro masakar harsashi daga cikin wata bindiga kirar pistola a jihar Ogun.

Lindaikeji ta rahoto cewa Janai Sunday ya harbi kansa a hannu, a cewar hukumar tsaro ta Amotekun reshen jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Yan Arewa Mazauna Jihar Imo Tare da Filewa Mutum Daya Kai

Amotekun
Wanda Ake Zargi Dan Kungiyar Asiri Ne Ya Dana Wa Kansa Harsashi A Lokacin Da Ya Ke Kokarin Sarrafa Bindiga. Hoto: @lindaikeji.
Asali: Twitter

Bindigar "Pistol ta fashe bisa tsautsayi, hakan yasa ya samu munanan rauni a hannunsa na hagu," a cewar rundunar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda aka kama wanda ake zargin

Kwamandan Amotekun na Ogun, CP David Akinremi (murabus), ya ce Jinai Sunday da wasu 'yan kungiyar asiri ta Aiye' suna wurin taronsu a wani daji da ke kan hanyar Kauyen Obada-Owode, karamar hukumar Imeko-Afon na Jihar Ogun ne a lokacin da abin ya faru.

A cewar Akinremi, bayan jin karar harbin bindigan, shugaban Amotekun na Imeko-Afon, bayan samun bayannan sirri, ya tura jami'ansa suka kama wanda ake zargin da wani Adejare Kehinde.

Shugaban na Amotekun ya ce a yayin da ake musu tambayoyi, ta bayyana cewa Adejare Kehinde ne ya ke siyo musu bindigu a Jamhuriyar Benin.

An yi nasarar kama wani Ogundele Elijah, wanda aka fi sani da Ogun 07, wanda ya bayyana cewa ya taba zuwa gidan yarin Ilaro ya yi wata shida saboda laifin shiga kungiyar asiri, saboda bayannan da aka samu daga wadanda aka kama da farko.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da shugabar matan APC a Kogi ta tsallake harin 'yan bindiga

Jami'an na Amotekun sun ce suna cigaba da bibiyan sauran yan kungiyar.

'Ni Na Rika Yi Wa Yan Bindiga Magani,' Fasinjar Jirgin Kaduna Da Ya Samu Yanci Ya Magantu

A wani rahoton, Mustapha Imam, daya daga cikin mutanen da yan bindiga suka sace jirgin kasar Kaduna zuwa Abuja ya ce ya yi wa yan bindiga magani a lokacin da ya ke tsare a hannunsu.

A wani bidiyon da Tukur Mamu, mawallafin Desert Herald wanda ya taimaka wurin tattaunawa don ganin an sake su, fasinjan ya bayyana zamansa a hannun yan bindigan a matsayin 'lamari matukar muni'.

Imam, wanda ma'aikaci ne a jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto, ya ce ba zai yi wa makiyinsa fatan shiga halin da ya tsinci kansa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel