Ana cikin Shagalin Sallah, Wani Abin Fashewa Ya Yi Bindiga a tsakiyar Jama'a a Najeriya

Ana cikin Shagalin Sallah, Wani Abin Fashewa Ya Yi Bindiga a tsakiyar Jama'a a Najeriya

  • Mutane da dama sun jikkata da gas din gidan mai ya fashe ana cikin hada-hada a Kalaba, babbin birnin jihar Kuros Riba
  • Rahotanni sun nuna cewa wutar da ta kama sakamakon fashewar ta taba shaguna da gidajen da ke unguwar a titin Edibe Edibe
  • Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar, ASP Eitokpah Sunday Akata, ya ce an tura jami’ai zuwa wurin domin shawo kan lamarin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Calabar, Cross River - Yayin da musulmin Najeriya ke ci gaba da shagulgulan Sallah, an samu wata fashewar gas a gidan man Fokex a Kalaba, babban birnin jihar Kuros Riba.

Lamarin ya auku a gidan mai na Fomex da ke kan titin Edibe Edibe a karamar hukumar Kalaba ta Kudu, a safiyar ranar Asabar, inda ta lalata dukiya mai darajar miliyoyin Naira.

Kara karanta wannan

Amurka ta ji wuya: Trump ya cirewa Iran takunkumin man fetur

Cross River.
Taswirar jihar Ribas da ke Kudancin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yadda gas ya fashe a gidan mai a Kalaba

Daily Trust ta rahoto cewa gas din ya fashe ne da misalin karfe 9:40 na safe, inda shaidu suka bayyana cewa karfin fashewar ya girgiza gine-ginen da ke kusa, har wasu suka dauka kamar fashewar bam ne.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu asarar rayuka ba, amma mutane da dama sun jikkata sakamakon fashewar.

Rahoto ya nuna cewa an ba wasu daga cikin wadanda suka ji rauni a agajin gaggawa a shagunan sayar da magunguna na kusa, yayin da aka garzaya da wasu asibitoci domin karin kulawa.

Wuta ta yi barna a gidaje da shaguna

Mazauna yankin sun nuna damuwa kan yadda jami’an kashe gobara na jiha da na tarayya suka jinkirta zuwa wurin, har bayan fiye da awa guda da faruwar lamarin.

Gidan man yana cikin unguwa mai yawan jama’a, lamarin da ya sa fashewar ta shafi shaguna da gidaje da dama, inda mazauna da ‘yan kasuwa suka tsere domin tsira da rayukansu.

Kara karanta wannan

Yaki ya yi zafi, Amurka ta fara neman $200bn don ci gaba da farmakin Iran

A yayin da jami’an agaji ba su iso ba, an ce wasu bata-gari sun yi anfani da damar wajen sace kayayyaki daga shagunan da abin ya shafa.

Rahotanni sun bambanta kan abin da ya haddasa fashewar. Wasu mazauna yankin sun zargi cewa wata kila wani kwastoma ne ya yi waya kusa da wurin zuba gas.

Sai dai wani mekanike mai suna Ekpenyong Sam, wanda ke aiki a kusa da wurin, ya danganta lamarin da matsalar lantarki ko kuma lalacewar kayan aiki, in ji Vanguard.

Hukumar kwana-kwana.
Motocin da ake amfani da su wajen kashe gobara Hoto: Anadolu
Source: Twitter

‘Yan sanda sun dauki mataki

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar, ASP Eitokpah Sunday Akata, ya ce an tura jami’ai zuwa wurin domin shawo kan lamarin.

Ya kara da cewa ana kokarin hada kai da jami’an kashe gobara, ciki har da na Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN), domin dakile gobarar da kuma dawo da tsaro a yankin.

Wuta ta kama a filin jirgin saman Legas

A wani rahoton, kun ji cewa gobara ta tashi a wani bangaren filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke jihar Legas.

Kara karanta wannan

Gobara ta tilasta wa jirgin yakin Amurka gudu wa daga yakin Iran

Sai dai an bayyana cewa gobarar ta takaita ne a wani ɓangare na tsohuwar tashar jiragen sama wanda ake gyarawa domin daidaita shi da sababbin ka’idoji.

Hukumar FAAN ta kwantar da hankulan fasinjoji da ke kai komo a filin jirgin, inda ta ce babu wanda ya rasa ransa sakamakon gobarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262