Tsofaffin Sojojin Najeriya Sun Fito kan Tituna, Sun Haifar da Matsala ga Gwamnati
- Tsofffin sojojin Najeriya sun yi zanga-zanga a Abuja, suna zargin Hukumar Fanshon da biyan su kuɗin fansho ƙasa da abin da aka amince da shi
- Sun ce an amince da yi ƙarin har zuwa kashi 80% ga sojojin Najeriya a karkashin gwamnati mai ci, amma su b su ga komai ba
- Masu zanga-zangar sun buƙaci a sake lissafa kuɗin fanshonsu bisa ƙa’idojin da aka amince da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsofaffin sojojin Najeriya sun gudanar da zanga-zanga kan zargin biyan su kuɗin fansho ƙasa da abin da ya kamata a rika biyansu, sun toshe kofar shiga hukumar fanshon soji a Abuja.
Sojojin, wadanda suka yi ritaya sun buƙaci a gaggauta sake lissafa hakkokinsu bisa ƙarin albashin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince wa sojojin da ke aiki.

Source: Facebook
Tsofaffin sojoji sun fito zanga-zanga
Daily Trust ta ce masu zanga-zangar, ƙarƙashin jagorancin Laftanar Kanal Innocent Azubuike, mai tsara ayyukan Ƙungiyar Tsofaffin Sojojin Najeriya, sun isa hedikwatar Hukumar Fanshon Sojoji da ke Abuja a safiyar Talata.
Sun zargi hukumar da amfani da tsarin lissafin fansho da ya rage kaso mai yawa na ƙarin kuɗin da aka yi masu.
Da yake magana yayin zanga-zanga, Azubuike ya ce an amince da ƙarin albashi daga 30 zuwa 80% ga sojojin da ke bakin aiki.
Dalilin zanga-zangar tsofaffin sojoji
Ya yi zargin cewa hukumar ba ta yi amfani da tsarin karin albashin tsaye wajen ƙara kuɗin fanshon da tsofaffin sojojin ke karɓa ba, maimakon haka ta yi amfani da wata hanyar lissafi da ta rage musu hakkokinsu.
Azubuike ya ce:
“Mun samu amincewar shugaban ƙasa kan ƙarin alawus ɗin da ya biyo bayan karin da aka yi wa rukunan mukamai daban-daban.”
“Amma lokacin biyan wannan ƙarin, Hukumar Fansho ba ta bi tsarin da aka amince da su ba.”
Ya bayyana cewa tsofaffin sojojin sun garzaya Ma’aikatar Tsaro a watan Agusta domin neman a saka su cikin ƙarin da ya shafi albashi, bayan sun gano cewa tun farko an cire su daga cikin waɗanda za su amfana.
A cewarsa, ma’aikatar ta amince da cewa an yi kuskuren cire su, sannan ta saka su cikin tsarin ƙarin da aka amince da shi.
Sai dai ya zargi Hukumar Fanshon Sojoji da bullo da wata hanyar lissafi da ta rage tasirin ƙarin, duk da cewa an riga an ƙayyade kuɗin fanshon kowane tsohon soja bisa matsayinsa da shekarun hidimarsa kafin ya yi ritaya.
Azubuike ya ce akwai kusan tsofaffin sojoji 100,000, yana mai cewa yana da takardun da ke nuna bambance-bambancen da ake zargi a lissafin kuɗin fanshonsu.

Source: Facebook
Tsofaffin sojoji sun nuna ɓacin rai
Wani tsohon soja,Duru Augustine, ya ce zargin rage kuɗin fanshon ya sa tsofaffin sojojin suka ji kamar an ci amanarsu bayan sun kwashe shekaru suna yi wa ƙasa hidima.
Augustine ya ce:
“Gaskiya, gaskiya, abin yana da muni. A cikin ƙasarka, a riƙa mu’amala da kai kamar bawa.”
Ya jaddada cewa saɓanin ya shafi yadda ake aiwatar da ƙarin kuɗin fanshon da aka amince da shi, wanda tsofaffin sojojin suka yi fafutukar ganin an ba su bayan sun gano cewa an cire su daga tsarin tun farko.

Kara karanta wannan
Kakar miliyoyin matasa ta yanke saƙa, an fadada shirin tallafin rage talauci a Najeriya
Tinubu ya yi karin kudin fansho
Kun ji cewa Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara biyan ƙarin kuɗaɗen fansho ga ma'aikatan da suka yi ritaya da ke ƙarƙashin tsarin DBS.
Ƙungiyar ƴan fansho ta tabbatar da cewa an fara biyan ƙarin na kaso 20% cikin 100% ga ma'aikatan da suka ajiye aikinsu.
Asali: Legit.ng

