Jerin kasashen da su ka fi fama da talauci a Duniya

Jerin kasashen da su ka fi fama da talauci a Duniya

A jerin Kasashen da su kowane fama da talauci a Duniya, Kasashen Afrika ne a kan gaba. Kasar farkon da ke wajen Afrika da za a fara cin karo da ita, ita ce Haiti. Majalisar dinkin Duniya ta fitar da wannan rahoto kwanaki.

Jerin kasashen da su ka fi fama da talauci a Duniya
Ana fama da matsanancin talauci a Yankin Afrika

A jerin dai ba a kawo irin su Kasar Sudan ta kudu da Yemen ba saboda halin tashin hankalin da Kasashen ke ciki.

1. Kasar Central Africa

Jamhuriyyar Kasar Central Africa ce kan gaba wajen fama da tsananin talauci inda sama da kashi 90% na kasar ke fama da yunwa da rashin muhalli. Kasar na fama da tsananin kazanta da matsalar rashin aikin yi.

KU KARANTA: Najeriya na cikin kasashen da ke asarar jama'arta saboda talauci

2. Kasar Burundi

Kasar Burundi tana cikin wani mawuyacin hali inda sama da kashi 90% na kasar ba su da abinci kuma ba su iya mallakar $2 a duk rana ta Allah. Yanzu haka dai mutane da dama sun bar Burundi sun koma wasu Kasashen.

3. Kasar Congo

Kasar Congo tana gaba a wannan jeri duk da irin albarkatun da Allah yayi mata. Mutanen da ke more rayuwa a Kasar Congo ba su wuce kashi 1% cikin 100 ba. Bayan nan kuma kasar na cikin inda su ka fi hadari a Duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel