Shari'ar El Rufa'i Ta Kara Zafi, an Tabo Maganar Kwace Kadarorinsa a Kotu

Shari'ar El Rufa'i Ta Kara Zafi, an Tabo Maganar Kwace Kadarorinsa a Kotu

  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da ya shigar domin hana ICPC ƙwace kadarorinsa
  • Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta ce ƙarar ta saba tsarin shari’a, kasancewar El-Rufai ya shigar da makamantanta a wasu kotuna a kasar nan
  • Ya nemi diyyar Naira biliyan 1 da kuma Naira miliyan 100 na kuɗin shari’a, yana mai cewa barazanar ƙwace kadarorinsa na iya tauye haƙƙoƙinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar domin hana ICPC da wasu hukumomi daskarar da asusun bankunansa ko ƙwace kadarorinsa.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik ce ta yanke hukuncin a ranar Alhamis, inda ta bayyana cewa ƙarar ta zama cin zarafin tsarin shari’a.

Kara karanta wannan

Atiku ya magantu kan tsadar kayan noma, ya fadi mafita tare da sukar Tinubu

Malam Nasir El-Rufa'i
Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i. Hoto: Bello El-Rufa'i
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa kotun ta amince da hujjojin waɗanda ake ƙara cewa El-Rufai ya shigar da makamantan ƙorafe-ƙorafe a Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) da kuma Babbar Kotun Tarayya.

Bukatun El-Rufa'i a kotu

El-Rufai ya shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/368/2026 a ranar 24 ga Fabrairu, 2026, ta hannun babban lauya Oluwole Iyamu.

A ƙarar, ya nemi kotu ta hana ICPC, EFCC, DSS da Babban Lauyan Tarayya ɗaukar matakin daskarar da asusun bankunansa ko ƙwace kadarorinsa.

Tsohon gwamnan ya kuma nemi umarnin wucin gadi da zai tilasta wa hukumomin su bar komai yadda yake har sai an kammala sauraron ƙarar.

Ya bayyana cewa kuɗin alawus ɗin da ya karɓa bayan kammala wa’adinsa na gwamnan Kaduna tsakanin 2015 da 2023 ba za a yi zargin cewa kuɗin haramtacciyar hanya ba ne ba tare da hujja ba.

Ya nemi diyyar N1bn

El-Rufai ya roƙi kotun ta tabbatar da cewa kadarorin da ya saya da kuɗin alawus ɗin mallakarsa ne bisa doka.

Kara karanta wannan

Yadda lauyoyi suka fafata a shari'ar Sheikh Lawal Triumph a kotun Kano

Ya kuma nemi umarnin dindindin da zai hana hukumomin daskarar da asusun bankunansa ko kwace kadarorinsa, ko kuma yin wani abu da zai hana shi mallakarsu.

Bugu da ƙari, ya nemi a ba shi Naira biliyan 1 a matsayin diyya kan abin da ya bayyana a matsayin barazanar tauye haƙƙoƙinsa na asali, jefa shi cikin damuwa da tashin hankali, da kuma ɓata masa suna.

Ya kuma nemi Naira miliyan 100 a matsayin kuɗin shari’a, ciki har da kuɗin lauyoyi da sauran kuɗin da aka kashe wajen shigar da ƙarar.

Matakin da kotu ta dauka

Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta bayyana cewa ba za a yi amfani da kotu wajen hana hukumomin da doka ta ba wa iko gudanar da ayyukansu ba.

Kotun ta kuma bayyana ƙarar a matsayin wadda ta dogara da hasashe kuma ba ta da isasshen tushe na shari’a.

Nasir El-Rufa'i a kotu
Lokacin da aka kai Nasir El-rufa'i kotu. Hoto: Uche Diala
Source: Facebook

Bugu da ƙari, ta ce ƙarar ba ta bayyana wani dalili na shari’a da zai sa a ci gaba da shigar da EFCC, DSS da Babban Lauyan Tarayya a matsayin waɗanda ake ƙara ba, don haka ta cire sunayensu daga cikin ƙarar.

Kara karanta wannan

Surutu ya ƙare, an yanke wa matashi hukunci kan taɓa martabar Annabi Muhammd SAW

An nemi a saki El-Rufa'i

A wani labarin, kun ji cewa Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, ya yi kira ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta magance ƙorafe-ƙorafen da suka shafi Nnamdi Kanu.

Atiku ya kuma nemi gwamnati ta yi bayani kan ci gaba da tsare Sheikh Sani Khalifa Zaria da Nasir El-Rufai, yana mai cewa ya kamata a yi amfani da doka cikin adalci a kowane lamari.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi wannan kira ne a Abuja yayin jawabin bikin Ranar ’Yancin Kan Najeriya, inda ya jaddada cewa ya kamata a mutunta wadanda aka kama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng