Shugaban Iran Ya Magantu kan Najeriya, Yana Son Karfafa Alaka da Kasarsa

Shugaban Iran Ya Magantu kan Najeriya, Yana Son Karfafa Alaka da Kasarsa

  • Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana bukatar karfafa alakar tattalin arziki, siyasa da al'adu tsakanin kasarsa da Najeriya
  • Ya ce akwai damammakin da har yanzu ba a yi amfani da su ba, wadanda za su taimaka wajen habaka hadin gwiwa da amfanar kasashen biyu
  • Jakadan Najeriya a Iran, Hamza Sallau, ya mika wa shugaban kasar wasikar shaidar nadinsa a matsayin jakada, yayin wata ganawa a birnin Tehran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Shugaban kasar Iran, Dr Masoud Pezeshkian, ya bukaci Najeriya da kasarsa su kara karfafa alakar tattalin arziki, siyasa da al'adu domin cin gajiyar damar hadin gwiwar da ke tsakaninsu.

Pezeshkian ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar wasikar shaidar nadin jakada daga sabon jakadan Najeriya a Iran, Ambasada Hamza Sallau, a wani taron diflomasiyya da aka gudanar a Tehran.

Kara karanta wannan

Na gaban goshin Tinubu ya fadi wanda suke shakka a 2027, ban da Atiku da Obi

Hamza Sallau da Masoud Pezeshkian
Hamza Sallau na mikawa Masoud Pezeshkian wasika a Tehran. Hoto: Iran Government
Source: Facebook

Radio Nigeria ya wallafa cewa mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Najeriya, Oluwafemi Adeniyi, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a a Abuja.

Iran na son karfafa alaka da Najeriya

Pezeshkian ya jaddada kudurin Iran na gano sababbin hanyoyin hadin gwiwa da Najeriya domin bunkasa dangantakar diflomasiyya da samar da moriyar juna ga kasashen biyu.

Ya ce akwai bukatar kasashen su zurfafa tattaunawa da hadin gwiwa a fannoni daban-daban domin cimma manufofin da suka sanya a gaba.

Martanin gwamnatin Najeriya

A nasa bangaren, Sallau ya isar da sakon gaisuwar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga takwaransa na Iran da al'ummar kasar.

Jakadan ya sake tabbatar da kudurin Najeriya na karfafa dangantakarta da Iran, inda ya bayyana kasuwanci, noma da kiwon lafiya a matsayin muhimman bangarorin da ya kamata kasashen biyu su kara yin hadin gwiwa a kansu.

Gwamnatin Iran ta wallafa a shafinta cewa ya ce hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da karfafa alakar kasashen biyu.

Kara karanta wannan

An kama mutumin da ke sa mata a mota ya masu bidiyo tsirara

Sallau ya yaba da yadda Najeriya da Iran ke goyon bayan tsarin hadin gwiwar kasa da kasa, yana mai cewa ya kamata a bai wa Kwamitin Hadin Gwiwa na Najeriya da Iran muhimmanci.

Ya bayyana cewa kwamitin na da rawar da zai taka wajen gano hanyoyin hulda da za su amfani kasashen biyu, tare da karfafa dangantakar diflomasiyya da tattalin arziki da ake da ita.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a jihar Jigawa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Kasashen biyu sun sake jaddada kudurinsu na fadada hulda a bangaren siyasa, karfafa hadin gwiwar hukumomi da kuma inganta alakar jama'arsu.

Mika wasikar shaidar nadin jakadan ya tabbatar da amincewa da Sallau a matsayin cikakken jakadan Najeriya mai wakilci na musamman a Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Iran ta kai wa Amurka hari

A wani labarin, kun ji cewa rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta ce ta kai hari tare da lalata na'urar gargadin farko ta Amurka da ke kasar Bahrain.

Rundunar ta ce harin ramuwar gayya ne kan harin sama da Amurka ta kai kan wata hasumiyar sadarwa a yankin Sirik, kusa da mashigar ruwan Hormuz.

A gefe guda, Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa zai kai hari kan Iran ne kawai idan bukatar hakan ta taso.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng