Ta caka wa mijinta wuka bayan ya mata dan-banzan duka

Ta caka wa mijinta wuka bayan ya mata dan-banzan duka

Jami'an 'yan sanda na hukumar a jihar Legas, sun kama wata malamar makaranta mai suna Abimbola Olamide sakamakon laifin sokawa mijinta Dare Akinbola, wuka da ake zargin ta dashi, inda ta kashe shi har lahira a gidan su dake Ikorodu a jihar Legas.

Ta caka wa mijinta wuka bayan ya mata dan-banzan duka
Ta caka wa mijinta wuka bayan ya mata dan-banzan duka
Asali: UGC

Jami'an 'yan sanda na hukumar 'yan sandan jihar Legas, sun kama wata malamar makaranta mai suna Abimbola Olamide sakamakon laifin sokawa mijinta Dare Akinbola, wuka da ake zargin ta dashi, inda ta kashe shi har lahira a gidan su dake Ikorodu a jihar Legas.

Punch Metro ta samu labarin cewa matar da mijin sun samu sabani ne a ranar laraba, wanda ya kaisu ga dambe.

A cikin damben ne, Olamide aka ce ta soka ma mijin nata mai shekaru 28 a duniya wuka, inda ta kashe shi har lahira.

A wani video da aka dauketa inda take fadin yanda abun ya faru, matar mai yara biyu tace tayi hakan ne don kare kanta.

Da take magana da yarbanci, tace, "Ban kashe mijina da gangan ba. Yana dukana ne, har ya fasa kwanukan abinci a kaina. Ya saba dukana lokuta da yawa a baya, amma duk lokacin da yake dukana, sai dai in gudu in bar gidan.

Amma a wannan lokacin, ya rufe kofa ne don hana ni guduwa, ya danne ni kuma yana duka. Na rasa mataimaki. Kawai sai na dau wuka da na gani a kasa. Naso inyi amfani da wukar ne don tsorata shi. Sai na rike ta a hannuna, amma yaki kyaleni. Ni kuma nayi kuskuren kasheshi; bazan kashe mijina da gangan ba. "

DUBA WANNAN: MTN zata fara biyan diyyar sace wa jama'a katin waya

"Yan uwana sun ce in rabu dashi, amma naki saboda mijina ne na kuruciya kuma uban yarana biyu ne. Ya saba dukana; kowa ma ya sani, ina hakuri ne."

Maganganunta dai sun jawo cece ku cen jama'a a ranar Alhamis.

Wasu suna cewa ta fuskanci shari'a, wasu kuma suna cewa kare kanta tayi wanda zai zama abin dubawa ga doka.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng