Fasto na zargin wasu manyan na'ibansa biyu a coci da kwartaci da matarsa

Fasto na zargin wasu manyan na'ibansa biyu a coci da kwartaci da matarsa

- Wani fasto yayi ikirarin cewa matar sa tana cin amanar sa tare da mazaje biyu dake cocin sa

- Faston ya fadawa kotu cewa matar bata mutunta shi kuma ta kaurace masa tun shekaru biyar da suka wuce saboda haka yana son a raba auren

- Matar tasa ta musanta zargin da yake mata inda ta kuma roki kotun kada ta raba auren domin ita tana son minjinta

A yau Laraba ne wani fasto mai suna Joshua Ibeneme ya ziyarci kotun Igando a garin Legas inda ya bukaci a raba aurensa da matarsa, Uzoamaka wanda sukayi shekaru 21 tare saboda yana zarginta da aikata zina da wasu mambobin cocinsa guda biyu.

Faston yayi ikirarin cewa Ubangiji ya fadamasa idan bai sake ta zata ruguza masa coci ya kuma shaida wa kotu cewa duk lokacin daya dawo daga tafiya sai yaransa su rika fada masa cewa maza suna zuwa suna daukar mahaifiyarsu kuma daga baya su dawo da ita gida a mota.

Fasto ya zargi matarsa da cin amanar aure, ya nemi kotu ta raba aurensu

Fasto ya zargi matarsa da cin amanar aure, ya nemi kotu ta raba aurensu

"Mata na tana cin amana na tare da mambobin coci na guda biyu, wani bisof da deacon. Dukkansu biyu suna ta yadda zancen ga sauran yan cocin inda suke alfari cewa mata ta ce ta bukaci su kusance ta."

DUBA WANNAN: Mai dakina na tura hotunan tsiraicinta ga kartin banza

Duk wannan na faruwa ne a yayinda she faston yayi ikirarin cewa matar tasa ta kwaurace masa har na tsawon shekaru biyar. "Duk lokacin da nayi kokarin kusantar ta sai ta rika kawo min dalilai daga baya ma ta dena kwana daki daya dani.

"Amma tana kwanciya ta mambobin coci na," inji faston.

Faston mai shekaru 53 ya kara da cewa matar tasa ta dade tana cin mutuncinsa cikin mutane inda take rika fadawa al'umma cewa baya iya tabuka komi a matsayinsa na da namiji. Ya kuma ce tana zarginsa da yin lalata da mata da ke zuwa neman shawarwari wajensa.

A bangarenta, matar tasa mai shekaru 45 musanta zargin cewa tana cin amanarsa da wasu mazaje. Ta kuma shaida wa kotu cewa mijin nata baya iya biya mata bukata kusan tsawon shekaru biyar da suka wuce amma duk da haka tace tana kaunarsa kuma ta roki kotu kada ta raba auren.

Alkalin kotun, Mr Akin Akinniyi ya bukaci ma'auratan su cigaba da zama lafiya kuma ya dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Mayu inda zai yanke hukunci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel