Bidiyo Ya Nuna Yadda Aka Kama Wani Dalibi Dan Najeriya a Burtaniya Dauke da Tsabar Kudi $8.5m

Bidiyo Ya Nuna Yadda Aka Kama Wani Dalibi Dan Najeriya a Burtaniya Dauke da Tsabar Kudi $8.5m

  • Hukumomi a kasar Burtaniya sun dura gidan wani dalibi dan Najeriya, inda suka gano tsabar kudi da suka kai $8.5m
  • Kudaden da aka gani cikin nau'ikan daloli daban-daban an ajiye su ne a cikin wani akwati, kamar yadda yake a wani bidiyo
  • Mutumin da aka kaman yana magana da daya daga cikin harsunan Najeriya, ya kuma bayyana cewa shi dalibi ne a kasar

Burtaniya - Wani bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta ya nuna lokacin da hukumomin kasar Burtaniya suka shiga gidan wani dalibi dan Najeriya, suka bankado wasu kudade masu yawa.

An ruwaito cewa, an kama dalibin ne da wasu daloli a cikin akwati, yawansu ya kai akalla $8.5m.

Bidiyon, wanda wani yanki ne na ayyukan kakkabe ta'addanci a Burtaniya, ya nuna dalla-dalla yadda aka dura gidan dalibin dan Najeriya da kuma yadda aka gano kudaden da ya boye.

Kara karanta wannan

Rikicin Makiyaya da Manoma Ya Barke, An Yi wa Kauyuka 10 Kaca-kaca a Jihar Kano

Hukumomin sun shiga gidan dalibin ne, da nufin bincike, sai kawai suka gano kudade a daure cikin wani akwati da aka boye.

An kama wani dan Najeriya da kudade
Bidiyo Ya Nuna Yadda Aka Kama Wani Dalibi Dan Najeriya a Burtaniya Dauke da Tsabar Kudi $8.5m | Hoto: Obakpee Isaac Osaheni
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Watakila kudaden harkallar haramun ne

A cewar bidiyon, akwai yiwuwar kudaden da aka gano na aikin ta'addanci ne, damfara ko kuma mallaki ne da wani dan Najeriya mai tafiyar da harkallar miyagun kwayoyi a Burtaniya.

Jim kadan aka ga wani matashi dan Najeriya ya shigo, inda ya nemi a bashi damar daukar littafinsa amma aka hana shi.

Daga nan dalibin ya fara kiran waya yana magana da harshen Yarbanci.

Shin kudaden nan da 'yan siyasa ne?

Ba a dai bayyana ko kudin mallakin daliban bane, ko kuma shi ake zargi da adana kudi masu yawan da suka wuce misali.

Wasu 'yan Najeriya na kan ra'ayin cewa, watakila da ne ga wani fitaccen dan siyasan Najeriya da ya saci kudi ya tsallaka dasu kasar waje.

Kara karanta wannan

Wani abu sai gayu: Takalmin gayu mai siffar mutum ya bar jama'ar intanet baki bude

Ya zuwa yanzu dai, kama 'yan Najeriya da kudaden da ake zargin na sata ne ko na wata harkallar da bata dace ba.

Bayyana sauya fasalin kudi a Najeriya na ci gaba da jawo cece-kuce a kasar, kuma hakan ya kai ga bankado kudade da yawa.

Babban bankin Najeriya ya yi karin haske kan nau'in kudaden da za a sauya da kuma yiwuwar kirkirar sabon nau'in kudi.

Hakazalika, ya yi bayani kan cece-kuce da ake yadawa kan cire rubutun Ajami a jikin kudin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel