Maganin Gargajiya Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane a Ondo

Maganin Gargajiya Ya Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane a Ondo

  • Rundunar 'yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da mutuwar mutane akalla uku bayan shan wani maganin gargajiya
  • Mutanen sun sha maganin ne yayin gudanar da bikin gargadin da ake kira "Ibogne" a yankin Akoko kudancin jihar
  • 'Yan sanda suna cigaba da bincike kan lamarin tare da bayyana halin da wani mutum da ya sha maganin yake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ondo - Rundunar 'yan sandan jihar Ondo ta fara gudanar da bincike biyo bayan mutuwar mutane biyu saboda shan maganin gargajiya.

Police
Yan sanda na bincike kan mutuwar mutane 2 bayan shan maganin gargajiya. Hoto: NIgerian Police Force
Asali: Facebook

Rahotanni da ke fitowa sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a yankin Ipe Akoko da ke karamar hukumar Akoko da ke kudancin jihar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 13 a Abuja, sun nemi N900m kudin fansa

Yadda mutanen suka mutu

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutanen sun mutu ne a ranar Lahadi da ta gabata yayin da na ukunsu ya ke kwance a asibiti.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton da jaridar the Guardian Nigeria ta wallafa ya nuna cewa mutanen sun je garin ne domin halartar wani bikin gargajiya da suke kira da "Ibogne".

An bayyana Alex Ojulewa da Samuel Alonge a matsayin wadanda suka mutu yayin da Audu Johnson yake kwance a asibiti rai a hannun Allah.

Faruwar lamarin ya jefa al'ummar garin cikin rudani kasancewar daya daga cikin mutanen ya zo ne daga Abuja domin halartar bikin.

Jawabin kakakin 'yan sandan jihar

Kakakin 'yan sandar jihar Ondo, Funmilayo Odunlami, ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce an kai rahoton faruwar lamarin ga jami'ansu.

Ta kuma kara da cewa a halin yanzu rundunar 'yan sandar suna cigaba da bincike domin gano kan lamarin da ɗaukan mataki, cewar jaridar Leadership

Kara karanta wannan

Miyagu sun tafka ɓarna, sun yi garkuwa da fasinjojin jirgin ruwa a Najeriya

Mai maganin gargajiya ya damfari wata mata

A wani rahoton kuma, kun ji cewa wata dattijuwa ‘yar shekara 86 mai suna Madam Alimot ta hadu da dan damfara da ya damfare ta miliyan 19.

Wanda ake zargin makaho ne da ke bayar da maganin gargajiya mai suna Owolabi Adefemi, kuma bayan damfararta ya kwanta da diyar ta har da jikarta don yi mata magani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel