Duniya kenan: Yadda uwa ta haifi jariri a cikin jirgin sama ta jefar dashi bandakin jirgi

Duniya kenan: Yadda uwa ta haifi jariri a cikin jirgin sama ta jefar dashi bandakin jirgi

  • Wata mata ta haifi santalelen jaririnta, amma ta jefar dashi a cikin jirgi saboda wasu dalilai da ba a sani ba
  • Wannan lamari ya faru ne a wata kasa a nahiyar Afrika kuma tuni aka gano wacece wannan mata
  • Yanzu haka dai an kwantar da ita da jaririn a asibiti kafin daga bisani a ci gaba da bincike kan wannan lamari

Mauritius - A yayin da ake gudanar da aikin bincike domin duba lafiyar jirgi na yau da kullum, jami'an filin jirgin sama a Mauritius sun gano wani jariri da aka jefar a cikin kwandon sharan ban daki na jirgin sama na Air Mauritius.

Ana zargin wata mata ‘yar Malagasy a kasar Madagascar mai shekaru 20 da haihuwar sabon jaririn, kuma an kama ta da farko, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Yadda raken N50 ya jawo rikicin da ya kai ga zub da jini da garkame kasuwa a jihar Kwara

Da farko dai ta musanta cewa yaron nata ne amma an yi mata gwaje-gwaje wanda ya tabbatar da cewa ta haihu, kamar Premium Times ta tattaro.

Hoton jaririn da aka haifa a jirgi aka jefar a bandaki
Duniya kenan: Yadda uwa ta haifi jariri ta jefar a cikin sama | Hoto: nypost.com
Asali: Twitter

An garzaya da uwar da jaririn duka zuwa asibiti kuma hukumomi sun ce suna nan "lafiya."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matar 'yar Malagasy, wacce ta zo Mauritius a kan takardar izinin aiki na shekaru biyu, tuni aka sanya ta a karkashin kulawar 'yan sanda.

Za a yi mata tambayoyi bayan an sallame ta daga asibiti kuma za a tuhume ta da jefar da jariri, kamar yadda rahotanni suka ce hukumomin kasar sun yanke.

Jirgin na Air Mauritius, wanda ya taso daga birnin Madagascar a ranar 1 ga watan Janairu ya sauka a filin jirgin sama na Sir Seewoosagur Ramgoolam da ke wajen babban birnin Port Louis.

'Yan bindiga sun hallaka jariri dan wata uku tare da mutane da dama a Benue

Kara karanta wannan

An ci gaba da shagalin biki bayan an sako amaryar da aka sace a Filato

A wani labarin, 'yan bindiga sun harbe jariri dan wata uku kacal har lahira tare da wasu mutum 12 a hari daban-daban a wasu kauyukan karamar hukumar Guma, jihar Benue, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Yan bindigan sun bude wuta kan matafiya a hanyar Uikpam–Umenger da misalin karfe 3:00 na yammacin ranar Talata, inda suka kashe mutum biyar, cikinsu harda jariri, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Hakanan, sauran mutum 8 Din an kashe su ne a yankin Branch Ude da misalin Karfe 10:00 na daren ranar Talata (Jiya).

Asali: Legit.ng

Online view pixel