Za a Saki 'Wasu' da aka Kama kan Zargin Shirya Yi wa Tinubu Juyin Mulki
- Ministan tsaro ya ce za a saki wasu daga cikin mutanen da aka kama bisa zargin hannu a shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu idan ba su da laifi
- Ya bayyana cewa hukumomin tsaro na ci gaba da bincike domin tabbatar da cewa ba a yi wa mutanen da ba su da hannu a lamarin zargin karya ba
- Christopher Musa ya ce wadanda bincike ya tabbatar suna da hannu sosai a shirin ne kawai za a gurfanar da su a gaban kotu a hukunta su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya ce wasu daga cikin wadanda aka kama kan zargin shirya juyin mulki a Najeriya za a sake su idan binciken da ake gudanarwa ya nuna cewa ba su da wata hujjar da za a gurfanar da su a kai.

Kara karanta wannan
Ana shirin zaben 2027, an fito da abin da ya faru lokacin da aka shirya yi wa Tinubu juyin mulki
Musa ya bayyana hakan ne yayin wata hira da manema labarai, inda ya yi bayani kan dalilin da ya sa ba a gurfanar da wasu daga cikin wadanda aka kama ba.

Source: Facebook
Channels Television ta ruwaito cewa ya ce hukumomin bincike na daukar lokaci domin tabbatar da cewa ba a hukunta wanda ba shi da laifi ba.
“Don haka, idan ba ku da wani laifi, bayan an kammala bincike, za a sake ku. Wadanda ke da manyan laifi ne za a ci gaba da shari’arsu,”
In ji shi.
Ya kara da cewa:
“Mun dauki lokaci ne domin tabbatar da cewa duk wanda aka sake bai cancanci a hukunta shi ba. Wadanda za a gurfanar su ne wadanda suka kasance manyan masu hannu a lamarin,”
Ya ce Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA) na ci gaba da bincike kan lamarin.
An gurfanar da wasu a kotu
Ministan ya ce wasu daga cikin wadanda aka kama tuni an bincike su tare da gurfanar da su a gaban kotu, inda ya jaddada cewa yanzu lamarin yana hannun kotuna.
Ya ce:
“Ina ganin an bincike su. An kai su kotu, don haka har yanzu lamarin yana gaban kotuna. Ba a hannunmu yake ba; yana hannun kotuna.”

Source: Twitter
Janar Musa ya ce shirin juyin mulkin gaskiya ne, yana mai cewa wadanda suka shirya shi na da niyyar aiwatar da shi.
Ya bayyana wadanda ake zargin da cewa “wasu mutane ne da suka batar da tunaninsu”, yana mai cewa bai yi imanin cewa manufar shirin tana da alaka da siyasa ba.
Fadin dajin Sambisa a Borno
A wani labarin, mun ruwaito cewa Christopher Musa ya kare gwamnati kan yaki da rashin tsaro, yana mai cewa faɗin wuraren da ’yan ta’adda suka mamaye na kawo cikas.
Ya ce jami’an tsaro na samun nasarar ceto mutanen da aka yi garkuwa da su akai-akai, amma ’yan ta’addan kan shiga manyan dazuzzuka kafin jami’an tsaro su isa gare su.
Ministan ya ce dajin Sambisa yana da girman da ya kai na kasar Belgium, yana mai cewa irin wannan faɗin fili na kara wahalar da jami’an tsaro.
Asali: Legit.ng
