Satar Mai: Majalisar Dattawa Ta Bankado yadda Aka Wawure $300bn
- Najeriya ta dade tana fuskantar matsalar satar danyen mai a yankin Niger-Delta da ke Kudancin kasar nan
- Majalisar dattawa ta kafa kwamiti na wucin gadi domin gudanar da bincike kan matsalar satar man wadda ke jawowa Najeriya babbar asara
- Kwamitin da majalisar ta kafa ya fara gabatar da bincikensa inda ya gano makudan kudaden da suka yi batan dabo saboda satar mai
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kwamitin da majalisar dattawa ta kafa don binciken satar mai ya fara gabatar da rahotonsa.
Kwamitin na wucin gadin na majalisar dattawa na yin bincike kan satar man fetur da sauran ayyukan barna kan tattalin arziki a yankin Neja-Delta.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta ce Sanata Ned Nwoko, ne ya gabatar da rahoton yayin zaman majalisar dattawa na ranar Laraba, 5 ga watan Nuwamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Ned Nwoko wanda ke wakiltar Delta ta Arewa a majalisar dattawa shi ne shugaban kwamitin.
Me kwamitin majalisa ya gano?
Ned Nwoko ya bayyana cewa binciken da suka gudanar zuwa yanzu ya nuna babbar asarar kudaden shiga da ta haura dala biliyan 300 daga danyen man da aka fitar ba tare da an rubuta shi cikin lissafi ba tsawon shekaru.
A cewar rahoton, kwamitin ya ba da shawarar a tilasta bin ka’idojin kasa da kasa na auna man fetur a dukkan wuraren hakowa da tashoshin fitar da mai, rahoton ya zo a jaridar The Punch.
Ya ce ya kamata a tilastawa hukumar NUPRC ta sayi sababbin na’urorin zamani na auna mai, ko kuma a mayar da alhakin hakan ga sashen auna kaya na ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da zuba jari ta tarayya.
Sanatan ya kara da cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta kaddamar da tsarin tsaro ta fasahar zamani, ciki har da amfani da jiragen leken asiri marasa matuka don taimakawa jami’an tsaro wajen yakar masu satar man fetur.
An ba gwamnatin Najeriya shawara
Rahoton ya kuma ba da shawarar kirkirar asusu na musamman domin inganta horo, tsaro a cikin harkokin ruwa.

Source: Instagram
“Ya kamata gwamnatin tarayya ta kafa kotuna na musamman domin gaggauta tuhumar masu satar mai da abokan hulɗarsu."
- Sanata Ned Nwoko
Ya ce ya kamata a ba kwamitin na musamman cikakken ikon bin diddigi, ganowa, da dawo da kudin da aka samu daga satar man fetur, a gida da kasashen waje.
Ya ce binciken da aka yi, ya nuna cewa akwai fiye da dala biliyan $22bn, $81bn da $200bn da ba a san inda suka tafi ba a lokuta daban-daban.
Majalisa ta dakatar da tantance minista
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawa ta dakatar da tantance sabon ministan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yake so ya nada.
Majalisar dattawan ta dakatar da shirin tantance Kingsley Udeh wanda Shugaba Tinubu ya dauko daga jihar Enugu don zama minista.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Rigima ta kaure a zaman Majalisar Wakilan Tarayya, an yi musayar yawu
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa an dakatar da tantancewar ne saboda rashin gabatar da rahoton tsaro daga hukumomin da abin ya shafa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

