Abin da Muka Sani kan Batun Yunkurin Kafa Hisbah a Plateau
- JNI reshen jihar Plateau ta ce babu wata ƙungiyar Musulmi da ta kafa ko ta sanar da shirin kafa Hisbah a Jos North.
- Sakataren JNI ya ce ce-ce-ku-cen ya samo asali ne daga hotunan da wasu mutane suka ƙirƙira ta amfani da fasahar AI
- Ya ce kafa Hisbah na buƙatar dokar da Majalisar Dokokin Jihar Plateau za ta amince da ita kafin ta zama halal
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jos, Plateau – Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) reshen Jihar Plateau ta musanta rahotannin cewa wata ƙungiyar Musulmi ta kafa Hisbah a karamar hukumar Jos ta Arewa.
Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin Jihar Plateau ta bayar da umarnin dakatar da ayyukan wata ƙungiya da ta ce tana gudanar da kanta a matsayin Hisbah a wasu sassan Jos ta Arewa.

Source: Facebook
JNI ta ce babu Hisbah a Jos ta Arewa
Da yake magana da Daily Trust a ranar Talata, 1 ga watan Satumban 2026, sakataren JNI a Plateau, Dr Salim Musa Umar, ya ce babu wata ƙungiyar Musulmi a jihar da ta sanar da shirin kafa Hisbah a Jos ta Arewa.
Umar ya ce batun ya samo asali ne daga kafafen sada zumunta, inda wasu mutane suka yi amfani da hotuna da aka ƙirƙira da fasahar Artificial Intelligence (AI) domin nuna cewa an kafa ƙungiyar Hisbah a yankin.
Ya ce hotunan sun haifar da ce-ce-ku-ce bayan da aka yaɗa su sosai a kafafen sada zumunta.
“Ina tabbatar wa jama’a cewa babu wata ƙungiyar Musulmi a Plateau da ta fito ta ce tana son kafa Hisbah. Babu wani abu makamancin haka, kuma ba a taɓa tattauna batun ba,” in ji shi.
‘Kafa Hisbah na buƙatar doka’
Sakataren JNI ya bayyana cewa ba za a iya kafa ƙungiyar Hisbah bisa son rai ba tare da wata doka da Majalisar Dokokin Jihar Plateau ta amince da ita ba.
Ya ce gwamnatin jihar ba ta samar da irin wannan dokar ba, don haka babu wani mutum ko ƙungiya da zai iya fito wa ya bayyana cewa ya kafa Hisbah a jihar.
Umar ya ce duk wata ƙungiya da za ta samu irin wannan matsayi dole ne ta kasance tana aiki ne bisa tsarin doka.
JNI ta nemi bincike kan lamarin
Umar ya yi kira ga gwamnatin Jihar Plateau da ta gudanar da cikakken bincike a duk lokacin da wani lamari da ya shafi addini ya taso, musamman idan yana da damar haifar da rikici tsakanin al'ummomi.
Ya ce bincike mai zurfi zai taimaka wajen gano gaskiyar lamura tare da hana yada bayanan da ka iya haddasa tashin hankali.
An gargadi masu amfani da kafafen sada zumunta
Sakataren JNI ya kuma yi kira ga masu amfani da kafafen sada zumunta da su guji ƙirƙira ko yaɗa bayanan da ka iya haifar da rashin fahimta tsakanin al’ummomi.
Ya ce ya kamata jama’a su tabbatar da sahihancin bayanai kafin su yaɗa su, musamman batutuwan da suka shafi addini da tsaro.
Ce-ce-ku-cen da ya shafi zargin kafa Hisbah a Jos North ya ci gaba da haifar da muhawara tsakanin mazauna jihar, musamman a kafafen sada zumunta da tsakanin al’ummomin yankin.

Source: Original
Dalung ya yi magana kan batun Hisbah a Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa Solomon Dalung, ya yi kira ga gwamnatin jihar Plateau da ta fito fili ta bayyana hujjojin zargin ayyukan Hisbah da ta ce an gudanar ba tare da izini ba a Jos.
Dalung ya ce umarnin da gwamnan jihar ya bayar na dakatar da ayyukan Hisbah da ba a san da su ba bai kamata a mayar da shi wata muhawara tsakanin Kirista da Musulmi ba.
Asali: Legit.ng


