Timpire Sylva yace kazafi Hukumar EFCC tayi masa
– Tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa Timpire Sylva yace karya Hukumar EFCC ta ke yi masa
– EFCC ta bayyana cewa ta maidowa Timpire Sylva gidajen sa har guda 48 da ta karbe a da
– Tsohon Gwamnan yace gidaje uku kadai ya mallaka a Abuja
Tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Mista Timpire Sylva yace Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa tayi masa kage.
Kwanakin nan ne Hukumar ta EFCC ta bayyana cewa ta maidawa tsohon Gwamnan gidajen sa da ta karbe a baya, zamanin mulkin Shugaba Jonathan.
Sai dai Gwamnan yace sharri kawai EFCC ta ke masa, bai mallaki wannan uban gidaje ba. EFCC tace gidajen Timpire Sylva da ta karbe a baya guda 48 ne, sai dai ta maida masa kayan sa. Sylva yace wannan maganar karya ce mai ban mamaki, kuma kawai an kirkire ta ne domin a bata masa suna.
KU KARANTA: Zaben Edo; PDP za ta je Kotu
The Cable ta rahoto Timpire Sylva yana cewa wannan abu bai masa dadi ba, kuma ‘yan adawa ne suka kirkiro wannan zance, Idan ba haka ba, ta ya za a tado maganar shekaru uku da suka wuce, bayan kuma ba shi ya mallaki gidajen nan ba.
Tsohon Gwamnan na Jihar Bayelsa Timpire Sylva dai yace yanzu haka ya sa lauyoyin sa da su maka kara Kotu domin a fito da gaskiya, domin ya wanke kan sa. Timpire Sylva ya rike Gwamnan Jihar ta Bayelsa ne bayan Shugaba Dakta Goodluck Jonathan.
Asali: Legit.ng