Abin da Muka Sani kan Zargin Ziyarar Manyan Ƴan Bindiga Gidan Sanata a Arewa

Abin da Muka Sani kan Zargin Ziyarar Manyan Ƴan Bindiga Gidan Sanata a Arewa

  • An yada wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ake zargin ya nuna ’yan bindiga daji a gidan sanata
  • Binciken da aka yi ya gano cewa an haɗa bidiyoyin mutane daban-daban guda biyu, kuma babu wata hujja da ta nuna mutanen ’yan fashin daji ne
  • An tabbatar da cewa mutanen bidiyon ’yan kasuwa ne da suka kai wa Sanata Shehu Buba Umar ziyara bayan dawowarsu daga aikin Hajji a 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Mutane da dama sun yi ta wani bidiyon da ke zargin ’yan fashin daji sun ziyarci sanatan Najeriya ƙarya ne.

An gano cewa wani bidiyo ya nuna cewa an yi amfani da shi wajen nuna wasu baƙi a wajen wani sanatan Najeriya a matsayin “manyan ’yan bindiga.”

Ana zargin ƴan bindiga sun ziyarci gidan sanata
Mutanen da aka yi ta yada bidiyonsu wai sun je gidan sanata. Hoto: @ZagazOlamakama.
Source: Facebook

Bidiyon da ake yadawa

Kara karanta wannan

Ana tsoron ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ‘yan NYSC 15 a hanyar zuwa Abuja

Wani mai amfani da kafar sadarwa, D English Alhaji ne ya yaɗa bidiyon sosai a Facebook da sauran kafafen sadarwa yana ikirarin cewa ya nuna wasu fitattun ’yan fashin daji suna “hutuwa” a gidan wani sanata da ba a bayyana sunansa ba.

Rubutun da aka sanya tare da bidiyon ya ce:

"Wadannan wasu manyan ƴan bindiga ne domin ziyara a gidan sanata."

Bidiyon ya jawo martani sosai a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka nemi a bayyana sunan sanatan.

Daga baya wata kafar yaɗa labarai ta wallafa batun bidiyon ba tare da tabbatar da sahihancin ikirarin ba.

Binciken da aka gudanar

Sai dai binciken gaskiya da PRNigeria ta gudanar ya tabbatar da cewa wannan ikirari ƙarya ne kuma bidiyon yana ɗauke da bayanan da aka karkatar.

Binciken ya gano cewa an samar da bidiyon ne ta hanyar haɗa wasu bidiyoyi guda biyu da ba su da alaƙa da juna.

Sashe na farko na bidiyon ya nuna wasu maza sanye da kayan gargajiyar Arewa, suna zaune a wani gida mai kyau suna tattaunawa da harshen Fulatanci.

Bincike ya nuna cewa mutanen da ke cikin wannan ɓangaren sun fito ne daga Akwanga, Nasarawa, kuma ba su da alaƙa da mutanen da ke cikin sashe na farko.

Kara karanta wannan

2027: Rundunar ’yan sandan Kano ta aika da gargaɗi mai zafi ga ’yan daba

Cikakken bincike ya tabbatar da cewa an ɗauki sassan bidiyon biyu ne a wurare daban-daban, kuma mutane daban-daban ne suka bayyana a cikinsu.

Saboda haka, babu wata hujja da ke tabbatar da cewa bidiyon biyu suna nuna abu guda ko kuma an ɗauke su a lokaci guda.

Duk da cewa an ga wata jaka mai ɗauke da kuɗi ko kaya a ɗaya daga cikin wuraren, binciken ya ce hakan kaɗai ba hujjar aikata laifi ba ce.

Wasu na ganin bakin sun je gidan Shehu Buba ne
Sanata Shehu Buba daga jihar Bauchi. Hoto: Senator Shehu Buba.
Source: Facebook

Abin da ya kai mutane gidan sanata

Ƙarin bincike ya gano cewa mutanen da ke cikin bidiyon farko mahajjata ne da suka kai wa Sanata Shehu Buba Umar ziyara a shekarar 2023 bayan dawowarsu daga aikin Hajji.

Sanata Shehu Buba Umar shi ne ke wakiltar mazabar Sanatan Bauchi ta Kudu a Majalisar Dattawan Najeriya.

An gano mutanen da suka kai ziyarar a matsayin ’yan kasuwa mazauna Kaduna, Alhaji Isa Usman da Alhaji Abubakar Bula.

Har ila yau, ba a gano wata hujja da ke danganta ɗaya daga cikin mutanen biyu da fashin daji, ta’addanci ko wani aikin laifi ba.

Kara karanta wannan

VeryDarkMan: Dan Tiktok ya nuna wa 'yan sanda tsaurin ido bayan sun gayyace shi

Barrister Musa Oga, wani mataimaki ga Sanata Buba, ya tabbatar da cewa bidiyon ya nuna mahajjata suna kai wa sanatan ziyarar girmamawa a shekarar 2023.

Ya bayyana bidiyon da aka yaɗa a matsayin wani ɓangare na yaƙin neman bata sunan sanatan, wanda yake ganin an shirya shi ne saboda dalilai na siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

An taba zargin Sanata Buba kan ta'addanci

A baya, an ji cewa jami'an DSS sun fara binciken Sanata Shehu Buba bisa zargin alaka da rikakken dan ta'adda Abubakar Idris.

An gano alamun alaka tsakanin Sanatan da Abubakar bayan hadiminsa Yahaya Ibrahim ya biyawa dan ta'addan aikin hajji.

Zuwa yanzu, an cafke Abubakar Idris, sannan an mika rahoto kan Sanata Shehu Buba ga shugaba Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.