Kididdigar Masana ta Nuna Fiye da Mutum 1,500 ne Suka Ɓace a Jihar Yobe

Kididdigar Masana ta Nuna Fiye da Mutum 1,500 ne Suka Ɓace a Jihar Yobe

  • Hukumar agaji ta Red Cross ta bayyana cewa tana kan bin sawun mutane fiye da 1,500 da suka bace a jihar Yobe
  • Kungiyar agajin ta ce a fadin Najeriya akwai fiye da mutum 17,000 da iyalansu ba su san inda suke ba
  • Rashin sanin makomar wadanda suka bacen yana jefa iyalansu cikin matsanancin halin kaka-ni-kayi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Damaturu, Jihar Yobe - Hukumar Agaji ta Red Cross ta Kasa da Kasa (ICRC) ta bayyana cewa tana ci gaba da bin sawun korafe-korafen mutane fiye da 1,500 da suka bace a jihar Yobe.

Wannan na zuwa ne a yayin da iyalan mutanen ke ci gaba da zama cikin fargaba da rashin tabbas kan halin da 'yan uwansu ke ciki.

Shugaban ofishin ICRC na Damaturu, Syed Rashid Hassan, shi ne ya bayyana hakan a garin Damaturu yayin wani taro na tunawa da Ranar Mutanen da Suka Bace ta Kasa da Kasa ta shekarar 2026.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun samu Naira biliyan 7 na kudin fansa cikin shekara 1 a Najeriya

Yadda mutane suka yi ta bata a Yobe
Taswirar jihar Yobe a Arewa maso Gabashin Najeriya
Source: Original

Mutane fiye da 17,000 ne suka bace a Najeriya

Hassan ya bayyana cewa wannan adadi na jihar Yobe bangare ne kawai na mutane fiye da 17,000 da hukumar ke bin sawun batan nasu a fadin Najeriya.

A cewarsa, fiye da rabin mutanen da aka rahota batansu yara ne a lokacin da lamarin ya faru, kamar yadda rahoton Daily Trust ya fada.

Ya kuma kara da cewa wannan adadi wani bangare ne kawai na ainihin adadin mutanen da suka bace a fadin kasar, domin da yawa ba a kai rahotonsu ba.

Hassan ya bayyana cewa zuwa karshen shekarar 2025, cibiyar sadarwa ta Family Links Network ta hukumar Red Cross ta yi rajistar mutane fiye da 513,000 da suka bace a fadin duniya.

Sakamakon rikici da kuma matsalar batan jama'a

Babban jami'in ya bayyana batun batan mutane a matsayin daya daga cikin mafi tayar da hankali da kuma cutarwa mai matukar tasiri da ke fitowa daga rikicin ta'addanci, yanayin rikice-rikice, abubuwan da suka shafi bala'i da kuma hijira.

Kara karanta wannan

Bill Gates ya fadi hadarin AI zai haifar a duniya a shekaru masu zuwa

Ya ce illar batan mutum ba ta tsayawa kan wanda ya bacen kadai ba, tana shafar iyayensa da sauran danginsa ta hanyar jefa su cikin matsalolin damuwa, halin rashin kudi, tsarin shari'a da ma zamantakewa.

Hukumar ICRC tana amfani da cikakken tsari domin tallafa wa iyalan da abin ya shafa, tare da hadin gwiwar kungiyar Red Cross ta Najeriya da hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki.

Yadda mutane suka yi ta bata a Yobe
Wasu daga wadanda ta'addanci ya shafa a Arewa. Hoton nan misali ne kawai | Hoto: AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Shugaban na ICRC ya ce kungiyar tana kokarin hana rarrabuwar iyali da batan mutane, da sake hada iyali, da gano makomar wadanda suka bace, da kare mutuncin mamata, da kuma inganta tsarin adana bayanan gawawwakin da ba a shaida su ba.

Shirin tallafa wa iyalan wadanda suka bace

Hassan ya bayyana cewa hukumar ta kaddamar da wani shirin tallafi a Damaturu domin taimaka wa iyali wajen rage radadin rashi da halin da suke ciki sakamakon batan 'yan uwansu.

A halin yanzu, fiye da iyali 50 ne suka samu tallafi ta hanyar wannan shirin da aka kaddamar, kamar yadda Red Cross ta shaida.

Jami’in na ICRC ya yi kira da a kara zage dantse wajen neman mutanen da suka bace domin ba wa iyalansu amsoshin da suke bukata.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun rutsa fitaccen ɗan kasuwa a masallaci bayan sallar Isha'i

Haka zalika, ya bukaci a samar da ingantattun dokoki da cibiyoyi na kasa, da suka hada da tsarin binciken magunguna da shari'a, da matakan sanin halin da mutane suka fada.

Jihar Yobe na daga jihohin Arewa maso Gabas da rikicin ISWAP da Boko Haram ya shafa, inda aka samu hare-hare da dama.

Wanda ya tantance Salisu Ibrahim, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng