Boko Haram: Mutanen kananan hukumomin Borno 4 na guduwa zuwa Yobe, Hukumar yan sanda
- Hukumar yan sanda ta bayyana damuwarta kan yadda mutanen Borno ke shiga Yobe
- A cewarta, an fara daukan sunayen yan gudun hijran amma ba duka ba saboda yawansu
Sakamakon hare-haren da yan bindiga ke kai musu kulli yaumin, mazaunan kananan hukumomin jihar Borno hudu sun yi gudun hijra zuwa jihar Yobe, hukumar yan sanda ta bayyana.
A cewar hukumar yan sandan Yobe, kananan hukumomin da mutane suke guduwa sune Gubio, Magumeri, Kaga da Konduga, Thisday ta ruwaito.
A jawabin da kakakin hukumar yan sandan, Dungus Abdulkarim, ya saki, ya bayyana cewa ana ganin ayarin mutane daga Gubio, Magumeri, Kaga da Konduga suna gudun Hijra jihar Yobe.
Yace: "Ana kyautata zaton suna gudun hijra ne daga muhallansu sakamakon hare-haren da wasu yan bindiga ke kai musu suna kwashe musu kayan abinda da dukiya."
"Hukumar a kokarinta ta dauki sunan masu gudun hijra 2000 don tabbatar da tsaro, amma mutane da yawa na gudun hijran har yanzu."
"Masu gudun hijran suna zama yanzu a kananan hukumomi irinsu Geidam, Tarmuwa da Gujba a jihar Yobe."
"Hakazalika kauyukan Isori, Kuka Reta, Kasesa da Kalallawa dake makwabtaka da Damaturu."
A cewar Abdulkarim, "Hukumar ta kaddamar da bincike kan dalilin da ya sa ake gudun hijran."
DUBA NAN: Shugaba Buhari ya tsawaita wa'adin IGP Adamu da watanni 3
KU KARANTA: Olonisakin, Buratai, Ibok-Ete Ibas da Siddique za su zama Jakadu a kasashen waje
A bangare guda, kungiyar ta'addan Boko Haram ISWAP, masu lakani da Jamā'at Ahl as-Sunnah lid-Da'wah wa'l-Jihād, sun ragargaza motoci biyu da kungiyar ta kwato daga yan sandan Nigeria.
A wani jawabi da kungiyar ta saki wanda SaharaReporters ta gani ranar laraba, sun kwaci motocin ne yayinda kungiyar ta kai hari wani chek point din yan sanda a hanyar Maiduguri-Chabal-Magumeri a jihar Borno.
Kauyen Chabal a karamar hukumar Magumeri yana da kilo mita 22 daga tashar Maimalari, 7 na marabar sojojin Nigeria a Maiduguri.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng