Hadimin Gwamna Ya Saduda, Ya Fito Ya ba Davido Hakuri
- Babban hadimin Gwamnan Edo kan kafafen sadarwa, Apostle Kassy Chukwu, ya ba Davido da al’ummar jihar hakuri kan kalaman da ya yi a baya
- Chukwu ya ce kalaman nasa ra’ayinsa ne na kashin kansa, ba umarnin Gwamna Monday Okpebholo ko gwamnatin jihar ba
- Ya tabbatar wa Davido cewa ko yaushe zai samu tarba a Edo, yana mai cewa al’ummar jihar masu son baki ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Edo - Babban mataimaki na musamman kan kafafen sadarwa na zamani ga Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, Apostle Kassy Chukwu, ya ba mawaki David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, da mazauna jihar hakuri kan wasu kalaman da ya yi a baya.
Chukwu ya bayyana cewa kalaman da ya yi, wadanda suka nuna cewa bai kamata Davido ya yi tsammanin zai yi wasa a Edo a lokacin mulkin Okpebholo ba, ra’ayinsa ne na kashin kansa, kuma gwamnan ko gwamnatin jihar ba su ba shi izinin yin hakan ba.

Kara karanta wannan
Shin da gaske gwamnatin Edo ta hana Davido shiga jihar bayan kin ba gwamna hakuri

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a wani bidiyo da jaridar THEWILL NEWSPAPER ta wallafa a shafinta na X ranar Asabar, 22ga watan Agustan 2026.
Chukwu ya ce kalaman nasa sun biyo bayan martanin da ya yi da kansa kan wata magana da ya ce Davido ya yi game da ’ya’yan gwamnan. Ya bayyana cewa bai yi bidiyon ne a matsayinsa na jami’in gwamnati ba.
“Ban yi wancan bidiyon a matsayina na wanda aka nada a gwamnati ba, kuma ban yi bidiyon ne bisa umarnin gwamnan jihar Edo ko da izininsa ba. Na yi bidiyon ne a matsayina na dan gwamnan da ya ji haushi saboda maganar da aka yi a bidiyon cewa ya kamata ’ya’yan gwamnan su ji kunyar mahaifinsu,” in ji Chukwu.
Chukwu ya nemi afuwar Okpebholo
Chukwu ya kuma nemi afuwar Okpebholo kan duk wata matsala ko kunya da kalamansa suka iya jawo masa, yana mai jaddada cewa gwamnan ba ya goyon bayan tashin hankali, barazana ko zalunci.
“Ina so na ba mai girma Sanata Monday Okpebholo, gwamnan jihar Edo, hakuri kan duk wata kunya da kalamaina suka iya jawo masa. Gwamnanmu mai son zaman lafiya ne kuma ba ya amincewa da tashin hankali ko barazana ko zalunci,” in ji shi.
Hadimin gwamnan ya kuma ba al’ummar Edo hakuri, yana mai cewa bai kamata a dauki kalamansa a matsayin ra’ayin daukacin mutanen jihar ba.
Ya bayyana mutanen Edo a matsayin masu son baki da kuma karbar mutane, tare da nuna nadama ga duk wanda kalamansa na baya suka bata wa rai.
“Kalamina, a ra’ayina na kashin kaina, ba su wakilci ra’ayin dukkan mutanen Edo ta kowace hanya ba. Mutanen Edo mutane ne masu kauna kuma masu karbar baki. Ina so na ba duk wani dan Edo da ya ga bidiyona a matsayin rashin mutunci kuma abin da ba za a amince da shi ba hakuri. Ina cewa na yi matukar nadama,” in ji shi.

Source: Facebook
Ya tabbatar wa Davido samun tarba a Edo
Da yake magana kai tsaye da Davido, Chukwu ya bukaci mawakin da ya yi watsi da kalamansa na baya, yana mai tabbatar masa cewa za a yi masa tarba a jihar Edo.
“Ina ba duk wani dan Edo mai kishin alheri da kuma dan uwana Davido hakuri. Ina son ka. Don Allah ka yi watsi da kalamina na baya. Edo na son ka kuma, tabbas, ana maraba da kai gida a ko da yaushe, a kowace rana, a jihar Edo. Ka ji dadin zuwa jihar Edo,” in ji shi.
Batun hana Davido shiga Edo
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Jihar Edo ta musanta cewa ta hana fitaccen mawakin Afrobeat, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, shiga jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa na jihar, Kassim Afegbua, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Asali: Legit.ng

