Yan Gida Daya Mutum 4 da Karensu Sun Bakunci Lahira bayan Cin Abinci Mai ‘Guba’
- Gwamnatin Kogi ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike bayan mutuwar wasu yan gida daya da wani karensu a Kogi
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa mutane huɗu daga gidan ɗaya sun mutu ne bayan sun ci amala a Ihima, ƙaramar hukumar Okehi
- Kwamishinan Yaɗa Labarai ya ce gwamnati na jiran sakamakon bincike, tare da gargadin jama'a kada su yi gaggawar yanke hukunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ihima, Kogi - Mutane huɗu daga gida ɗaya sun mutu bayan sun ci amala a Ihima, da ke ƙaramar hukumar Okehi a jihar Kogi.
Rahotanni sun bayyana cewa karen gidan shi ma ya mutu bayan ya ci daga cikin abincin da mutanen suka ci.

Source: Original
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Sadarwa na Kogi, Kingsley Fanwo, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, cewar Punch.
Matakin da gwamnatin Kogi ta dauka
Bayan faruwar lamarin, gwamnatin Kogi ta bayar da umarnin gudanar da bincike nan take domin gano musabbabin mutuwar.
Ya ce Gwamnan Kogi, Ahmed Ododo, ya umarci Kwamishinan Lafiya da ya fara cikakken bincike kan lamarin.
Gwamnan ya nuna matuƙar damuwa kan wannan mummunan lamari, tare da umartar Ma’aikatar Lafiya da ta binciki dalilan mutuwar.
Ya ce binciken zai mayar da hankali kan yiwuwar gubar abinci ko kuma gurɓacewar abincin da iyalin suka ci.
Binciken zai kuma tantance ko abincin da mamatan suka ci ya gurɓace, ko kuma wani yanayin lafiya ko muhalli ne ya haddasa mutuwar.
Gwamnan ya umarci hukumomin da abin ya shafa su binciki samfuran abincin da sauran hujjojin da ake da su bisa ƙa’idojin lafiyar jama’a.

Source: Facebook
Gwamnatin Kogi ta damu kan mutuwar kare
Fanwo ya ce gwamnati ta kuma damu da rahoton mutuwar karen gidan bayan cin abincin, yana mai cewa hakan zai kasance cikin abubuwan da za a bincika.
Ya ce Gwamnan ya umarci Ma’aikatar Lafiya da ta haɗa kai da sauran hukumomi da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cikakken bincike.
Gwamnatin za ta ɗauki matakan da suka dace na kare lafiyar jama’a bisa sakamakon binciken da za a gudanar.
Ta buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, tare da guje wa yin gaggawar yanke hukunci kan musabbabin mutuwar.
Fanwo ya ce ya kamata a jira binciken hukumomin da abin ya shafa kafin a tabbatar da ainihin abin da ya faru.
Ya kuma bayyana cewa Gwamna Ododo ya jajantawa iyalan mamatan da al’ummar Ihima bisa wannan babban rashi.
Almajirai 11 sun mutu a Kaduna
A baya, an ji cewa wasu almajirai 11 sun rasa rayukansu a wata mahaƙar ƙasa da ke kauyen Yar-doka a ƙaramar hukumar Kubau ta jihar Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa almajiran sun je wurin ne da nufin taimakon malaminsu, kwatsam ƙasa ta rufa kansu.
Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce an tura jami'ai domin fara bincike kan haƙiƙanin abin da ya afku.
Asali: Legit.ng

