Matsalar rashin abinci mai gina jiki ta kashe kananan yara 29 a jahar Gombe

Matsalar rashin abinci mai gina jiki ta kashe kananan yara 29 a jahar Gombe

Akalla yara 29 ne yunwa ta kashesu a jahar Gombe a sakamakon rashin samun ingantaccen abinci mai gina jiki daga watan Janairu zuwa watan Oktoban shekarar 2019, a yayin da aka garzaya dasu zuwa cibiyoyin kulawa da masu fama da cutar da yunwa.

Jaridar Blue Print ta ruwaito shugaban wata kungiyar dake kula da ingancin abinici a Najeriya (ANriN), Sulaiman Mamman ne ya bayyana haka a yayin wani taron masu ruwa da tsaki inda suka tattauna kan hanyoyin shawo kan matsalolin rashin abinci masu inganci.

KU KARANTA: Rikicin duniya da mai rai ake yin ta: Miji ya zargi matarsa da kwanciya da maigidansu

A yayin taron wanda kungiyar CISLAC da gidauniyar Aisha Buhari ta shirya a garin Gombe, Mamman yace daga watan Janairun 2019 zuwa Oktoba, an kwantar da kananan yara 5,029 a cibiyoyin kiwon lafiya guda 18 dake kananan hukumomi 4 a jahar, inda aka sallami 2,123 bayan sun samu sauki.

Haka zalika Mamman yace akwai iyayen da suka kwashe yara 273 daga cibiyoyin ba tare da wata dalili ba, yayin da yara 29 suka mutu a cibiyoyin, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito shi.

Shi ma a nasa jawabin, shugaban kwamitin majalisar dokokin jahar Gombe dake kula da kasafin kudi, Aliyu Usman Baba Manu ya bayyana damuwarsa game da matsalar rashin samun abinci mai gina jiki a jahar.

“Mun fahimci daga kokarin da gwamnan jahar Gombe yake yi, akwai alamu zai gwamnan zai taka rawar gani wajen kula da kiwon lafiya a jahar, saboda idan babu kyakkyawar lafiya, yaran ba zasu iya karatu ba. Haka zalika majalisa na da burin yin doka game da hakan.” Inji shi.

A wani labari kuma, a ranar Talata, 26 ga watan Nuwamba ne gwamnatin jahar Zamfara ta soke dokar da ta tilasta ma gwamnatin jahar Zamfara biyan tsofaffin gwamnoni miliyoyin kudade a matsayin kudin fansho, tare da haramta biyan gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel