Wata mata ta saci jariri saboda bata haifi da namiji ba

Wata mata ta saci jariri saboda bata haifi da namiji ba

Yan sanda a jihar Ekiti sun kama wata mata mai suna Mercy Momoh wacce ake zarginta da satar jariri dan watanni biyu a Ado-Ekiti, babban birnin jihar.

An kama Momoh wacce ta fito daga jihar Edo a ranar Asabar a gidanta da ke yankin Odo-Aremu, hanyar tsohon ofishin gwamna da ke babban birnin jihar.

Ta sace jinjirin daga mahaifiyarsa, Misis Funmilayo Sunday a ranar Juma’a da misalin karfe 1:00 na rana a sakatariyar jihar.

An tattaro cewa mai laifin ta dana wa mahaifiyar yaron tarko inda har ta bita zuwa sakatariyar jihar domin karban wasu kayan agaji da gwamnati ta ba wadanda ambaliyar ruwa ya cika da su.

Da suka isa wajen sai mai laifin ta tura mahaifiyar yaron ta siyo mata katin waya, sannan sai ta gudu da jaririn kafin mahaifiyar ta dawo.

Kakakin yan sandan jihar, Caleb Ikechukwu ya tabbatar da kama mai laifin a ranar Asabar, inda ya kara da cewar ana kan gudanar da bincike.

Da take zayyana, mai laifin tace ta saci jinjirin ne saboda tsananin sonta ga mallakar da namiji.

KU KARANTA KUMA: Shehu Sani ga Buhari: Gurfanar da Sowore gaban kotu zai bata maka suna

Mai laifin tayi ikirarin cewa sakamakon rashin haihuwar da namiji mijinta ya sake aure auren wata matar sannan ya koreta daga gidan shi.

Majiya ta bayyana cewa kwamishinan yan sanda, Amma Asuquo, ya yi umurni ga a binciki lamarin da kyau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel