Allah yayi: Najeriya da Kasar China sun kulla alaka mai girma a Duniya
A makon nan ne mu ka ji cewa Kasar Najeriya da kuma China sun shiga wata yarjejeniyar kudi. Idan za ku tuna hakan dai na zuwa ne kusan bayan shekaru 2 da kasashen su ka fara wannan magana har aka yi tunani maganar ta bi ruwa.
An cin ma yarjejeniya tsakanin babban bankin Najeriya CBN da kuma bankin mutanen kasar China PBoC inda Najeriya za ta amfana da Dala Biliyan 2.5. Wannan yarjejeniya zai kawo sauki wajen neman kudin kasar waje a Najeriya.
Darektan sadarwa na babban bankin Najeriya Isaac Okarafor ya bayyana cewa an rattaba hannu a Birnin Beijing na kasar China a yarjejeniyar tsakanin Gwamnan CBN Godwin Emefiele da kuma Takwaran sa na PBoC Dr. Dr. Yi Gang.
Wannan yarjejeniya za ta taimakawa China da Najeriya wajen tattalin kudin kasar wajen su, ban da kuma alakar kasuwanci da za a kulla tsakanin kasashen. Zai dai yi wa China saukin sayen albarkatun Najeriya kuma a taimakawa Najeriya.
KU KARANTA: Mata sun bada sharudan bada kuri'a a zaben 2019
Dama can kun ji cewa Najeriya ce kasa ta uku a Afrika da ta shiga wannan shiri da China bayan zuwan Gwamnatin Buhari. Kasar ta China za ta rika musayar kudin ta na Yuan da kuma Nairar Najeriya domin ayi kasuwancin kasa-da-kasa cikin sauki.
A makon nan dai Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa har yanzu fa akwai sauran aiki gaban sa a Najeriya. Shugaban kasar ya bayyana wannan ne a makon nan lokacin da yake hira a Rediyo a Kasar Amurka game da Boko Haram.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng