Kwamishina a Legas Ya Ajiye Aikinsa Saboda Rugujewar Wani Katafaren Gini

Kwamishina a Legas Ya Ajiye Aikinsa Saboda Rugujewar Wani Katafaren Gini

  • Kwamishinan tsare-tsare da raya birni a jihar Legas ya hakura, ya ajiye aikinsa saboda wasu dalilai
  • Ana yawan samun rugujewar gine-gine a jihar Legas, musamman daga bara zuwa tsakiyar wannan shekarar
  • Gwamnatin jihar Legas ta kafa kwamitin da zai bincike musabbabin yawaitar rugujewar benaye a jihar

Jihar Legas - A rahoton da muke samu, an ce kwamishinan tsare-tsare da raya birane na jihar Legas, Dakta Idris Salako ya ajiye aikinsa sakamakon yawaitar rugujewar gine-gine a jihar.

An ce kwamishinan ya shiga tashin hankali sosai yayin da ya kafa tarihi a matsayin kwamishinan da gini ya fi rugujewa a zamaninsa a jihar, PM News ta ruwaito.

A karkashinsa ne wani bene mai hawa 21 a Ikoyi ya rushe a 2021, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 50.

Kara karanta wannan

Na Gaji da Najeriya Ne: Yaro Mai Shekaru 14 da Aka Tsinta a Filin Jirgin Sama

Kwamishina Salako na jihar Legas ya ajiye aiki
Kwamishina a Legas ya ajiye aikinsa saboda rugujewar wani katafaren gini | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Na karshe da ya rushe ya kuma tunzura kwamishinan shi ne ginin bene mai hawa 7 na ranar Lahadin da ta gabata, wanda ya kashe mutane biyu suka mutu, Vanguard ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai, wata majiya ta yi zargin cewa kwamitin da gwamnatin jihar Legas ta kafa ce ta dakatar da Salako yayin da take nemo musabbabin rugujewar bene mai hawa 21 a Ikoyi a bara.

A bangare guda, kwamishinan yada labarai na jihar Legas, Gbenga Omotoso a wata sanarwa da ya cire a yau Litinin 5 ga watan Satumba ya ce gwamna Babajide Sanwo-Olu ya amince da ajiye aikin Dr. Idris Salako.

Bene Mai Hawa 7 Ya Ruguje, Ya Ritsa da Mutane a Legas

A wani labarin na daban kuma, bene mai hawa bakwai da ake tsaka da gininsa a titin Oba Idowu Oniru dake jihar Legas ya rushe inda ya ritsa da mutum shida.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shugaban 'yan sanda ya magantu kan yiwuwar yin zabe a shekara mai zuwa

Daily Trust ta rahoto cewa, babban sakataren hukumar again gaggawa ta jihar, Dr Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya tabbatar da faruwar lamarin a sa'o'in farko na ranar Lahadi.

Ya bayyana cewa, an fara kokarin ceto wadanda lamarin ya ritsa da su. Yace: "Bayan isa wurin da abun ya faru, wani bene mai hawa bakwai da ake ginawa ya rushe. Babu wanda ya samu rauni amma mutum shida ake gano ya murkushe kuma ginin ya hana su fitowa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel