Abubuwa 2 da Ƴan Najeriya Ke Buƙata Domin Fita Daga Kalubalen Rayuwa, Kashim Shettima

Abubuwa 2 da Ƴan Najeriya Ke Buƙata Domin Fita Daga Kalubalen Rayuwa, Kashim Shettima

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce abubuwa biyu ƴan Najeriya ke buƙata domin su fita daga kalubalen da ƙasar ke fuskanta
  • Ya ce har sai mutane sun ba gwamnati goyon baya tare da saka yaƙinin cewa komai zai gyaru ne Najeriya za ta shawo kan matsalolinta
  • Shettima ya yi wannan jawabi ne a Abuja, a wajen bikin kaddamar da cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta Najeriya a ranar Litinin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, a ranar Litinin, ya bukaci goyon bayan daukacin ‘yan Najeriya a kokarin da ake na magance kalubalen da ke addabar kasar.

Kashim Shettima ya yi magana kan kalubalen da Najeriya ke fuskanta
Shettima ya ba 'yan Najeriya shawarar hanyar fita daga kalubalen rayuwa. Hoto: @officialSKSM
Asali: Facebook

Gwamnatin Tinubu ta yarda akwai matsala

Kara karanta wannan

Mambila: An tona yadda aka nemi amfani da kaidin mata a yaudari wasu ministoci

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Shettima ya yi wannan jawabi ne a Abuja, a wajen bikin kaddamar da cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesa Bolaji Akinyemi ne ya kafa cibiyar wadda ke da nufin ba da gudummawa ga tsara manufofin kasashen waje da aiwatar da su a Najeriya.

Da yake jawabi a wajen taron, mataimakin shugaban kasar, ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta amince da cewa Najeriya na fuskantar kalubale.

"Abin da 'yan Najeriya ke bukata" - Shettima

Rahoton jaridar Tribune Online ya nuna cewa Shettima ya samu wakilcin Hakim Baba Ahmed, mai ba shi shawara na musamman kan harkokin siyasa, inda ya ce:

“Wannan gwamnatin ta yarda da cewa muna fuskantar matsaloli, duk da hakan, muna da yakinin cewa Najeriya za ta fita daga kalubalen da take fuskanta.

Kara karanta wannan

Abacha ya karkatar da maƙudan kudi a mulkinsa? Buba Galadima ya fayyace gaskiya

"Abubuwa biyu muke da bukata; yakinin cewa komai zai daidaita da kuma goyon baya, abubuwan da suka taimake mu wajen fita daga manyan kalubale a baya."

Ya ce Najeriya na da karfin ikon magance matsalar talauci, abubuwan more rayuwa, bunkasa matasa da ba su ilimi.

Tinubu ya yi wa ƴan Najeriya tanadi?

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yi wa ƴan Najeriya albashir da irin tanadin da Shugaba Bola Tinubu ya yi masu.

Shettima ya ce domin tabbatar da cikar muradun gwamnatin Tinubu, shugaban ƙasar ya dukufa wajen ganin ya dawo da tsaro da zaman lafiya a jihohi ƙasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel