'Yan sanda sun damke wani mutum da ake zargi da safarar makamai da harsasai 299

'Yan sanda sun damke wani mutum da ake zargi da safarar makamai da harsasai 299

- Hukumar 'yan sandan jihar Cross River sun kama wani Cyprian Mbe da sunkin alburusai 299 a wata bakar jaka

- Sun fita sintiri ne, sai suka dakatar da mutane masu tafiya don su duba kayansu, a nan suka kama mutumin

- An gano cewa Mbe mai shekaru 52 yana safarar makamai a karamar hukumar Etung da makwabtan ta

Hukumar 'yan sandan jihar Cross River sun damki wani mutum mai shekaru 52 mai suna Cyprain Mbe, wanda ake zargin yana safarar miyagun makamai.

An kama shi lokacin da 'yan sanda suka fita sintiri yayin da suka dakatar da ababen hawa don su bincikesu a karamar hukumar Etung da ke jihar, The Nation ta wallafa.

Ana zargin Cyprain Mbe dan kauyen Bashia da ke karamar hukumar Boki da safarar makamai.

An kama shi a kwanakin karshen mako da curin alburusai guda 299 boye cikin wata bakar jaka.

KU KARANTA: Tashan wutan lantarki ta kasa ta lalace, sunayen jihohin da rashin wuta zai shafa

'Yan sanda sun damke wani mutum da ake zargi da safarar makamai da harsasai 299
'Yan sanda sun damke wani mutum da ake zargi da safarar makamai da harsasai 299. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Baka san darajar da ka kara a idon masu caccakarka ba, Ndume ga Jonathan

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Abdulkadir Jimoh ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Litinin a Calabar, inda yake cewa wanda ake zargin yana safarar makaman yaki ne a karamar hukumar Etung da kuma sauran kananan hukumomi da ke makwabtaka da su.

CP Jimoh ya bayyana yadda wanda aka kama yake da hannu dumu-dumu a safarar makamai a anguwanni don tayar da hankula.

Bayan kokarin kungiyar 'yan sa kai da suka yi sintiri, inda suka dakatar da mutane masu wucewa don bincike kaya, a nan suka samu nasarar damkarsa.

A cewarsa, 'yan sanda suna nan suna kara bincike a kan lamarin don su kara ganowa idan akwai wasu da ke killace da makaman, kuma za a yi gaggawar turas hi kotu don a yanke masa hukunci.

A wani labari na daban, wani dan jarida dan Najeriya, David Hundeyin ya bayyana yadda aka kirkiri Boko Haram a Najeriya, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Hundeyin ya zargi arewa da kirkirar muguwar kungiyar da yanzu ta girma ta fi karfin gwamnati, ya ce ya daina tausayawa wadanda ta'addancin ya shafa tun bayan ya yi bincike a kan yadda aka kirkiri kungiyar a arewa a 2019.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel