Rufin Gini Ya Rufto Kan Wani Gini Ba a Kammala a Jami'ar Jihar Taraba

Rufin Gini Ya Rufto Kan Wani Gini Ba a Kammala a Jami'ar Jihar Taraba

  • An samu asarar rai bayan rufin wani gini ya rufto a jami'ar jihar Taraba da ke birnin Jalingo, babban birnin jihar
  • Shaidun ganau ba jiyau ba sun bayyana cewa rufin ginin ya rufto ne sakamakon rashin yin amfani ɗa katoko mai ƙarfi wajen riƙe shi
  • Hukumar gudanarwar makaranta ba ta yi ƙarin haske ba saboda a cewarta aikin ginin ba ita ba ce ke gudanar da shi, wanu ɗan kwangila ne

Jihar Taraba - Aƙalla mutum ɗaya ne aka tabbatar da mutuwarsa tare da jikkata wasu bayan rufin wani gini ya rufto kan wani ginin da ba a kammala ba a jihar Taraba.

Jaridar Channels tv ta kawo rahoto cewa lamarin ya auku ne a harabar jami'ar jihar Taraba, da ke Jalingo babban birnin jihar a ranar Juma'a, 29 ga watan Satumban 2023.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan Bindiga Sun Ɗana Tarko, Sun Yi Garkuwa da Babban Jami'in Sojojin Najeriya

Rufin wani gini ya rufto a Taraba
Rufin ginin ya rufto ne a jami'ar jihar Taraba Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Meyasa rufin ginin ya rufto ƙasa?

Shaidun ganau ba jiyau ba wadanda mafiya yawansu ɗalibai ne da suka nemi a sakaya sunansu, sun bayyana cewa katakon da aka yi amfani da shi wajen riƙe rufin ba ya da ƙarfin da zai riƙe shi wanda hakan ya sanya ya rufto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar jami'in watsa labarai na jami'ar, Sanusi Sa’ad, aikin ginin ba hukumar gudanarwar makarantar ce ke tafiyar da shi ba, aikin na ɗan kwangila ne wanda mutumin da ya rasu ma'aikacinsa, domin haka ba zai iya yin ƙarin bayani kan lamarin ba.

Duk kokarin jin ta bakin ɗan kwangilar ko kuma sunan kamfaninsa ya ci tura har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Har yanzu dai rundunar ƴan sandan jihar ba ta ce komai ba a kan lamarin.

Bene ya rufto a Anambra

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Benue Ya Fusata Kan Sace Manyan Yan Siyasa a Jiharsa, Ya Ba Jami'an Tsaro Muhimmin Umarni

Wani ginin bene da ake gudanar da aikinsa ya rufto a Egbu Umuenem, a gundumar Otolo Nnewi, a ƙaramar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar Anambra.

Ginin ya rufto ne da daddare lokacin da ma'aikatan da ke aiki a wajen ke barci domin fara aikinsu gari na wayewa.

Katanga Ta Rufto Kan Wasu Yara

A wani labarin kuma, wata katanga ta rufto kan wasu yara a jihar Legas sakamakon ruwan sama da a ka tafka kamar da bakin ƙwarya.

Katangar da ta rufto kan yaran dai ta wani gida ne da ke makwabtaka da su a titin Alao, cikin Isawo a ƙaramar hukumar Ikorodu ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel