Gwamnatin Zamfara Ta Haramta wa Mutanen Ƙauyuka Sulhu da Yan Bindiga, An Ji Dalili
- Gwamnatin Zamfara ta gargadi mazauna jihar da su guji kulla sulhu da ƴan bindiga, tana mai cewa duk mai yin hakan ya yi gaban kansa ne kawai
- Gargaɗin ya biyo bayan kuɓutar kusan dattawa 40 daga Maradun da suka shiga daji domin yin sulhu da ƴan bindiga bayan an gayyace su
- shugaban ƙaramar hukumar Talatar Mafara, Yahaya Abubakar Yari ya bayyana cewa akwai yanayin da ake yin sulhu na hakika don ceton rayuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara – Gwamnatin jihar Zamfara ta sake bayyana matsayarta kan matsalar tsaro, inda ta gargadi al'ummar jihar da kada su riƙa shiga sulhu da ƴan bindiga masu garkuwa da mutane.
Ta ce duk wanda ya zaɓi yin sulhu da waɗannan masu aikata laifuffuka ya yi hakan ne da kansa, kuma gwamnati ba za ta ɗauki alhakin sakamakon hakan ba.

Kara karanta wannan
Matasa sun tura saƙo ga Bola Tinubu da 'yan bindiga suka ƙona garuruwa 7 a jihar Neja

Source: Facebook
BBC Hausa ta wallafa cewawannan sabon gargaɗi ya zo ne bayan rahotannin da suka nuna cewa wasu kusan dattawa 40 daga yankin Maradun sun shiga daji domin tattaunawa da ƴan bindiga, amma daga bisani suka samu kuɓuta daga hannunsu.
Gwamnatin Zamfara ta gargadi jama'a
A hirar da ta kebanta ga kafar, shugaban ƙaramar hukumar Talatar Mafara, Yahaya Abubakar Yari, ya bayyana cewa sulhu yana da ma'anarsa a wasu yanayi, amma ba a irin wannan matsala da ake fama da ita a Zamfara ba.
Ya ce a fahimtarsa, ana yin sulhu ne da ƙungiyoyin da suka ɗauki makami saboda wasu buƙatu ko korafe-korafe da suke ganin ba a biya masu ba, kamar masu tayar da ƙayar baya da ke neman wani hakki.
Sai dai ya ce halin da ake ciki da ƴan bindiga ya bambanta, domin abin da suke yi ya ta'allaka ne kan aikata manyan laifuffuka kamar garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa, satar dabbobi da kai hare-hare kan al'umma.
Muna kan bakarmu - Gwamnatin Zamfara
Shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa sboda wadannan daliai, bai kamata a ɗauki irin waɗannan masu aikata laifuffka a matsayin waɗanda za a zauna da su domin sulhu ba.

Source: Original
A cewar gwamnatin Zamfara, matsayarta bai sauya ba, kuma za ta ci gaba da ɗaukar matakan tsaro da haɗin gwiwa da hukumomin tsaro domin daƙile ayyukan ƴan bindiga.
Sannan ya roƙi mazauna jihar su guji ɗaukar matakan da ka iya jefa rayuwarsu cikin haɗari kamar yin gaban kansu wajen sulhu da yan bindiga.
Sojoji sun kori yan ta'adda a Zamfara
A baya, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun yi namijin kojari wajen tunkarar wasu masu dauke da makamai da ake zargin 'yan bindiga ne bayan sun kai masu hari kan wasu sojoji a jihar Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan masu tarin yawa sun kai harin amma an yi gaggawar tura wa sojojin karain dakaru daga sansanoni biyu da ke jihar bayan an dakile harin da aka tun da fari.
Rahotanni sun bayyana cewa harin da aka kai sansanin sojoji na FOB wanda ke karamar hukumar Bukuyyum da ke jihar Zamfara da Zummar ya gamu da tirjiyar jami'an tsaro da suka hana 'yan bindiga samu nasara.
Asali: Legit.ng
