'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki kan 'Yan Sanda, an Samu Asarar Rayuka

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki kan 'Yan Sanda, an Samu Asarar Rayuka

  • Wasu ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai harin ta'addanci kan jami'an tsaro na ƴan sanda a jihar Enugu
  • Miyagun ƴan bindigan sun farmaki ƴan sanda a wani shingen bincikensu da ke garin Achi a ƙaramar hukumar Oji River
  • Jami'an ƴan sanda uku da wani farar hula sun rasa rayukansu sakamakon ƙazamin harin da ƴan bindigan suka kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Enugu - Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai wani mummunan hari kan ƴan sanda a garin Achị, da ke ƙaramar hukumar Oji River a jihar Enugu.

Ƴan bindigan sun kashe ƴan sanda uku tare da wani farar hula guda ɗaya a ranar Talata, 15 ga watan Afrilu, 2025.

'Yan bindiga sun farmaki 'yan sanda a Enugu
'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda uku a Enugu Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ƴan bindiga sun farmaki ƴan sanda

Jaridar Vanguard ta ce mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun kai farmakin ne a wani shingen bincike da ke kusa da kasuwar Ozudaa, wadda ta shahara a cikin garin Achi.

Kara karanta wannan

Ana jimamin rikicin Plateau, 'yan bindiga sun hallaka mutane a Benue

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan sun kashe jami’an ƴan sandan guda uku da farar hular, maharan sun ƙone motar da jami'an tsaron ke amfani da ita wajen gudanar da ayyukansu na tsaro.

Wannan harin ya girgiza mazauna yankin tare da haddasa fargaba da tsoro a zukatan jama'a.

Har yanzu ba a samu cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru ba, domin rundunar ƴan sandan jihar Enugu ba ta fitar da wata sanarwa ko tabbatar da faruwar lamarin a hukumance ba.

Legit Hausa ta tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Enugu domin samun ƙarin bayani kan lamarin.

Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa yana cikin wani taro ne amma a tura masa saƙo ta wayarsa.

"Ina cikin wani taro ne, ka tura min saƙo ta waya."

- Kakakin ƴan sandan Enugu

Sai dai, kakakin ƴan sandan bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hare hare a Zamfara, sun tafka barna mai yawa

Ƴan bindiga sun yi ta'asa a Enugu

A wani bidiyo da ke ta yawo a kafafen sada zumunta, an ga gawarwakin jami’an ƴan sandan kwance a gefen hanya.

Yan sanda
'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda a Enugu Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Har yanzu ba a tabbatar daga wane ɓangare maharan suka shigo ba, ko daga Awgu ko daga ɓangaren Oji suka yi amfani da shi wajen ƙaddamar da harin.

Mutane biyu ƴan asalin garin Achi, Maxwell da Daniel, sun tabbatar da faruwar harin.

Sun ce lamarin ya girgiza su matuƙa, kuma sun bayyana cewa farar hular da aka kashe matashi ne wanda yake sananne a yankin, wanda ya kasance mai halin kirki da son zaman lafiya.

Mazauna yankin na kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro a yankin domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Ƴan bindiga sun kai hari a Benue

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Benue.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wuta kan jami'an tsaro, an samu asarar rayuka

Ƴan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Utopi da ƙe ƙaramar hukumar Otukpo, suka hallaka mutum bakwai tare da raunata wasu da dama.

Harin ya jefa mutanen yankin cikin fargaba, inda suka yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro kan su kai musu agajin gaggawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng