Ana Cikin Surutu, Gwamnati Ta Jero Kuɗin da Ake Turawa Kowane Sanata duk Wata
- Gwamnatin tarayya ta bakin hukumar raba kudin shiga watau (RMAFC) ta bayyana albashin da kowane sanata yake samu
- Hukumar ta karyata ikirarin da Sanata Shehu Sani ya yi na cewa kowane sanata na karbar N13.5m matsayin kudin gudanarwa a wata
- A cewar hukumar RMAFC, albashin sanatoci bai kai kudin da Shehu Sani ya fadi ba, yayin da ta yi bayanin abin da ake biyan a majalisu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar tattara kudaden shiga da kasafin kudi (RMAFC) ta yi karin haske kan albashin da 'yan majalisar dattawa ke karba a kowanne wata.
Hukumar RMAFC ta ce kowanne sanata daga cikin sanatoci 109 da ke a majalisar dattawa na karbar albashi da alawus na ₦1,063,860 a duk wata.
Shugaban RMAFC, M. B. Shehu, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya yi wannan karin hasken matsayin martani ga wani ikirari na Sanata Shehu Sani, inji rahoton Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"N14.25m ne albashin sanatoci" - Shehu Sani
Shehu Sani, wanda tsohon sanata ne daga Kaduna ya ce kowanne sanata na karbar kudin tafiyar da aiki a da ya kai N13.5m ban da N750,000.00 da hukumar RMAFC ke biya duk wata.
The Punch ta ruwaito Sanata Shehu ya ce hukumar RMAFC ba ta da wani karfin iko da tsarin mulki ya ba ta na tilasta albashi da alawus din da 'yan majalisar ke samu.
"Duk da haka, majalisar tarayya na kan warware wannan dambarwar da aka samu."
- In ji tsohon sanatan.
Hukumar RMAFC ta fadi albashin sanatoci
Shugaban RMAFC ya ce wasu alawus-alawus na yau da kullun ne yayin da wasu kuma na lokaci daya ne, yana mai cewa:
“Ana biyan alawus-alawus na yau da kullun tare da albashi yayin da ake biyan alawus na lokaci daya a dukkanin lokacin da bukatar hakan ta taso.
"Misali, alawus na kujeru, tebura da sauran kayan gida (N6,079,200) da alawus na sallamar aiki (N6,079,200) ana biyansu sau daya a shekaru hudu."
Hukumar RMAFC ta kara da cewa ana biyan kowane sanata N8,105,600 na alawus din sayen mota wanda ke zuwa matsayin rance da dan majalisar ke biya kafin barin ofis.
Nawa ne kudin sanatoci duk wata?
Hukumar ta bayar da bayanin albashi da kuma alawus da ake biyan kowane sata a duk wata kamar haka:
- Albashi - N168,866:70
- Kudin fetur da kula da abin hawa - N126,650:00
- Kudin biyan hadimai - N42,216:66
- Kudin biyan 'yan aikin gida - N126,650:00
- Kudin nishadi - N50,660:000
- Kudin ruwa, wuta da sauran ayyuka - N50,660:00
- Kudin jarida - N25,330:00
- Kudin sutura - N42,216:00
- Kudin kula da gida - N8,443:33
- Kudin ayyukan mazaba - N422,166:66
"An karawa sanatoci albashi" - Jaafar Jaafar
A wani labarin, mun ruwaito cewa fitaccen ‘dan jaridar nan daga Kano, Ja’afar Ja’afar ya yi ikirarin cewa an kara albashin da ‘yan majalisar tarayya suke karba.
Ja’afar Ja’afar ya yi wannan magana ne a shafukansa na sada zumunta inda ya yi ikirarin cewa sanatan da ake biya N13.5m a kowane wata, yanzu ya koma karbar N20m.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng