Malami ya yiwa dalibar shi dukan tsiya saboda taki amincewa tayi soyayya da shi

Malami ya yiwa dalibar shi dukan tsiya saboda taki amincewa tayi soyayya da shi

Abun al’ajabi da mamaki baya karewa a wannan zamanin da muke ciki, iyaye na tura yaransu makaranta domin koyo ilimi sai gashi ana samun wasu batagarin malamai da ke kokarin lalata tarbiyarsu ta hanyar kulla soyayya da su a makaranta.

Hakan ce ta kasance a wani labari da ya billo a kafofin sadarwa inda aka zargi wani malami da yiwa wata dalibarsa dukan kawo wuka saboda ta ki yarda tayi soyayya da shi.

Yayar dalibar ta makarantar sakandare na mata wato Gbaja Girls Secondary High School da ke Mushin ce ta fallasa abunda ya wakana a tsakanin kanwar tata da malamin makarantar.

KU KARANTA KUMA: Wani bawan Allah ya tsinci naira miliyan 9.7 a ATM sai ya mayar dashi cikin banki

Ta bayyana cewa malamin wanda aka ambata da suna Mista Kayode daga ajin SS1b ya yiwa kanwarta mugun duka kan zargin cewa tana tafiyar izza amma zancen gaskiya shine cewa ya doke ta ne don ta ki amsar tayin soyayyarsa.

Kalli bidiyon a kasa:

A wani labari na daban, mun ji cewa wata matar aure a jihar Delta ta bada labarin cin amanar da mijinta wanda suka yi shekaru tara tare yayi mata.

Matar mai suna Awele Ejiofor ta bayyana yadda mijinta mai suna Toby Onyekweli ya ce mata zai tafi jihar Borno kasuwancin shi amma sai ganin hotunan auren shi ta yi, kamar yadda jaridar Gistmania ta ruwaito.

Matar cike da matukar kunar rai ta bayyana hakan a shafinta na Facebook. Mijin nata a cikin jihar Delta ya nemi auren kuma aka daura bayan bai sanar da ita ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel