Jam’ian tsaron Najeriya na taimakawa yan kasan Sin masu hako madaina ba bisa ka’ida

Jam’ian tsaron Najeriya na taimakawa yan kasan Sin masu hako madaina ba bisa ka’ida

-Ankama yan kasan Sin guda takwas

-Ana hako ma'adanai na kimani bilyan biyar a kowani wata

-Mista. Lalong yayi barazanar canza shugaban yansandan Karamar hukumar Wase

Ministan ma’adanai na kasa,Kayode Fayemi, ya zargi jami’an tsaro da tamaikawa masu hako ma’danai ba a bisa ka’id ba a Najeriya.

Mista. Fayemi ya zargi su ne lokacin da yake zantawa da jami’an tsaro a kauyen Kampani zurak dake masarautar Bashar a karamar hukumar Wase inda aka kama masu hako ma’adanai guda 20, wanda ya hada da yan kasan Sin guda 20 a ranar Litinin

“Ance jami’an tsaro ke basu kariya. In bah haka mai yasa mutanen ku ke gadin wajen?”Inji ministan.

Jam’ian tsaron Najeriya na taimakawa yan kasan Sin masu hako madaina ba bisa ka’ida
Jam’ian tsaron Najeriya na taimakawa yan kasan Sin masu hako madaina ba bisa ka’ida

Legit.ng ta samu rahoton cewa jami’an tsaro na Special Taskforce Jos sun sa shingaye guda uku a hanya zuwa wajen kamfanonin hako ma’adanai dake jihar Jos.

KU KARANTA:Daliban sekandare guda 4 sun sace na’urar 'Laptop' na kimanin miliyan N1.4 a Jigawa

Mista Fayemi ya misalta masu hako ma’adanai ba a bisa ka’ida ba da cewa sune masu yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa.

“Irin wannan abun, ba ya faruwa a ko ina a duniya, saboda haka ba za mu yarda da irin wannan barnan a kasan mu ba.

Jam’ian tsaron Najeriya na taimakawa yan kasan Sin masu hako madaina ba bisa ka’ida
Jam’ian tsaron Najeriya na taimakawa yan kasan Sin masu hako madaina ba bisa ka’ida

Gwamnan jihar Jos, Simon Lalong a lokacin da yake jawabi sa, ya ce gwamnatin sa, za ta hukunta duk wani sarkin gargajiya da aka kama shi da hada kai da masu hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba.

Mista Lalong yayi barazanar canza shugaban yansandan Karamar hukumar Wase saboda zargin hada kai da masu hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba.

Lalong yace ana hako ma’adanai na kimanin biliyan biyar N5b a kowani wata.

Shugaban kungiyan cigaban masarauta Bashar, Zakari Mohammed ya bayyana wa ministan cewa akawai ma’adaina na kimanin biliyan N15 a ajiye a ma’aikatan hako ma’adanan.

Jam’ian tsaron Najeriya na taimakawa yan kasan Sin masu hako madaina ba bisa ka’ida
Jam’ian tsaron Najeriya na taimakawa yan kasan Sin masu hako madaina ba bisa ka’ida

Mohammed yace ayyukan masu hako ma’adanai ya lalata ruwan shan yan garin.

Kwamshinan ma’aikatan jin korafe-korafe na jihar Plateau, Musa Adamu, wanda dan garinne ya fada manema labarai cewa, akalla mutane goma suka rasa rayukan su ma cutar Cholera a garin saboda amfani da lalatace ruwa.

Wani matashi a unguwan, mai suna Usman Usman, yace suna karuwa da kamfanonin hako ma’adanai a garin sosai.

“A nawa ra,ayin suna taimaka mana sosai, ta dalilin su na gina gida kuma nayi aure .Na kan samu N30’00 zuwa N50,000 a cikin satin biyu ta dalilin wannan aikin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng