Sheikh Disina: Abin da ya sa na daina yin bikin Mauludi bayan na tashi mu na yi a da

Sheikh Disina: Abin da ya sa na daina yin bikin Mauludi bayan na tashi mu na yi a da

  • Ra’ayin Ibrahim Adam Disina ya canza a game da maulidi a shekarun baya
  • Shehin malamin ya alakanta canjin da ya samu da haduwa da malaman Izala
  • Kungiyar Izala tana cikin masu adawa da yin bukukuwan mauludin Annabi

Bauchi - Ibrahim Adam Omar Disina wanda malamin addinin musulunci ne a jihar Bauchi, ya yi rubutu a game da abin da ya canza masa ra’ayi kan maulidi.

A Facebook, Sheikh Ibrahim Adam Omar Disina ya bada labarin yadda ya yi watsi da maulidin Annabi Muhammad (SAW), bayan ya tashi su na yin bikin.

Babban malamin yake cewa a haife shi a garin Disina ne shekaru fiye da 40 da suka wuce, kuma da yake yaro, duka mutanen garinsu mabiya akidar darika ne.

Read also

Tsohon Shugaban Majalisa ya rubuta littafi, ya tona asirin Obasanjo na neman zarcewa a mulki

Mahaifan Dr. Ibrahim Adam Omar ne suka fara yin karatun boko a duk fadin garin Disina kamar yadda ya bayyana a shafinsa a ranar 19 ga watan Oktoba, 2021.

A lokacin da Sheikh Disina ya taso, Shehu Malam Adamuwa ne babban malamin da ke garinsu, kuma makarantarsa ce take shirya mauludi a wannan kauye.

Sheikh Disina
Dr. Ibrahim Disina Hoto: www.bbc.com
Source: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Malamin yake cewa an gina masallacin Izala na farko a Disina, jihar Bauchi ne a shekarar 1993. Saboda haka kafin nan sun dauka yin maulidi yana da kyau.

Da mu aka yin bikin maulidin a baya

"A wajejen shekara ta 1988 zuwa 1990 ina daga cikin wadanda ake gabatarwa don yin kasida daga Islamiyyar Malam Adamuwa lokacin bikin Mauludi."
"Marigayi Shehun Bamaina shine Babban Malamin da ke zagayawa gari gari tsakanin Bauchi da Jigawa don gabatar da tarukan Mauludi!! – Dr. Disina."

Read also

‘Yan Najeriya na fama da yunwa, talauci da rashin tsaro – Sheikh Dahiru Bauchi ya koka

Lamari ya canza salo

A wannan lokaci, taron maulidin ya kare ne a kan kasidu da ba mutane tarihin Annabi SAW. Sai dai daga baya abubuwan suna ta canza salo a wurare da-dama.

Bayan zuwa wannan malami garin Bauchi a 1990, sai ya hadu da malaman Izala, ya shiga neman ilmi gadan-gadan, daga nan ya rabu da akidar da yake a kanta.

A jawabin na sa, Disina ya kawo hujjoji bakwai da ke tabbatar da cewa bikin maulidi bai da asali a musulunci. Daga ciki yace sahaban Annabi SAW duk ba su yi ba.

Menene ra'ayin Ahmad Gumi a kan maulidi?

Kuna da labari cewa akwai wasu malamai da suke ganin cewa mauludi da ma kirismeti duk wasu bukukuwan bidi'a ne da aka kirkiro daga baya a addini.

Ahmad Gumi yana daga cikinsu, yace daga Annabi Adamu zuwa Muhammad (SAW), babu wanda ya san yaushe aka haife su, don haka babu dalilin yi masu biki.

Read also

Abun bakin ciki: Yadda ‘da ya kashe mahaifinsa a kan gona a jihar Gombe

Source: Legit Newspaper

Online view pixel