'Yan Sanda Sun Ayyana Neman Tsohon Dan Takarar Shugaban Kasa, Sowore Ruwa a Jallo
- Rundunar yan sanda ta umarci dakarunta su kama dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore a duk inda suka gan shi a jihar Legas
- Kwamishinan yan sandan jihar, Olorundare Jimoh ya ce sun samu labarin shirin da Sowore ya yi na tayar da zaune tsaye da sunan zanga-zanga
- Rahotanni sun nuna cewa yan kungiyar Take It Back Movement da Sowore ke jagoranta sun fito zanga-zanga amma yan sanda sun kore su
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - Rundunar 'Yan Sandan Jihar Legas ta ayyana dan gwagwarmaya kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.
Yan sanda sun dauki wannan matakin ne bisa zarginsa da yunkurin ta da zaune tsaye da hargitsi da sunan zanga-zanga a jihar Legas.

Source: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa a kwanakin baya, kwamishinan ‘yan sandan Legas, Olorundare Jimoh, ya gargaɗi Sowore da ya guji shirya zanga-zanga lam rusau da gwamnatin jihar ta aiwatar a unguwar Oworonshoki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sowore, jagoran “Take It Back Movement”, ya yi barazanar gudanar da zanga-zanga a makonnin baya domin nuna adawa da rusa gidajen da gwamnati ta yi da sunan shirin sabunta birni.
'Yan sanda sun tarwatsa zanga-zanga
Duk da gargaɗin da rundunar ta yi, magoya bayan wannan kungiya sun fito a ranar Litinin, sun fara gudanar da zanga-zangar lumana.
Sai dai jami’an ‘yan sanda na sashin tarwatsa tarzoma da na Rundunar Task Force sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar
Rahotanni sun bayyana cewa Sowore, mamallakin jaridar Sahara Reporters, bai halarci zanga-zangar ba, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Dalilin neman Sowore ruwa a jallo
Bayan jami’an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zangar, Kwamishinan ‘yan sandan, Jimoh, ya bayyana Sowore a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo, bisa zargin kokarin tada tarzoma da gangan.
“Ya shirya dukkan tsare-tsare don toshe hanya a kan gadar Third Mainland Bridge, wannan babban laifi ne mai tsanani.
"Abin da yake son yi shi ne jefa ga al’umma cikin kunci da wahala, musamman matafiya da ke amfani da hanyar. Ba za mu bari hakan ta faru ba.
"Mun kusa kama shi kuma duk inda ya shiga ya buya, za mu zakulo shi. Muna da bidiyo da ke nuna cewa ya sauka daga jirgi daga Abuja amma bai fito ba saboda tsoron kama shi.”
- CP Olorundare Jimoh.

Source: Twitter
Tuni dai aka jibge jami’an tsaro a manyan wurare a Legas, musamman a kan Gadar Third Mainland Bridge, domin hana duk wata zanga-zanga da ka iya haifar da cunkoson ababen hawa ko hargitsi a gari.
Sowore ya soki barazanar Trump
A wani rahoton, kun ji cewa dan gwagwarmayar nan, Omoyele Sowore ya soki barazanar shugaban Amurka Donald Trump ta turo sojoji su yi yaki a Najeriya.
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele ya gargadi ‘yan Najeriya da su yi hattara da barazanar shugaba Donald Trump domin babu alheri a ciki.
Sowore ya bayyana cewa kalaman Trump na iya burge wasu, amma tarihi ya tabbatar da cewa irin mamayar Amurka ba sa kawo mafita.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


